Me ya sa ba a iya yi mana bayanin wasu abubuwan da ke ba mu tsoro ba?
Me ya sa ba a iya yi mana bayanin wasu abubuwan da ke ba mu tsoro ba?
Tsoron maɓallai da wani matashi dan Afirka ke yi tsawon rayuwarsa na bayyana yadda kayan amfanin yau da kullum kan iya zama kurkuku mai ban ta’ajibi.
4 awanni baya

A littafin George Orwell na 1984, jarumi Winston Smith yana da tsoron beraye. Babu wani abu da zai iya razana shi - ba wai azabtarwa ta zahiri ba, har ma da mutuwa da ke kallonsa a fuska.

Shirin ‘Daki na 101’, inda fursunoni ke fuskantar fargabar da ke tsakaninsu, ya samo asali ne daga fahimtar Orwell game da yanayin tsoro na sirri, kuma sau da yawa ba za a iya bayyana shi ba.

“Abin da ke gurgunta fahimtar daidaiton mutum na yau da kullun na iya kama wani abin dariya, idan ma ba na rashin hankali ba.

Wa wajen James*, maɓallai su ne wannan abin tsoro.

Ba kamar yawancin mutanen da ke kallon maɓallai a matsayin ƙananan abubuwa na roba ko ƙarfe da ba a wani damu da su ba, waɗanda ake amfani da su wajen daure tufafi a jiki, a koyaushe James na ɗauke da tsoro da ƙyama, ga wannan abu na amfanin yau da kullun.

A likitanci, ana kiran yanayin da saurayin ya shiga da ‘koumpounophobia’, wanda ke cikin nau’ikan tsoro da ba a saba gani ba, kuma suke shafar kusan mutane 75,000 kowace shekara.

"Duk lokacin da na taɓa maɓalli, sai na ji wani yar a jikina," in ji shi. "Ba na son ganin komai da ke da shi da kuma dauke shi."

James ya tuna lokacin da ya fara fuskantar hakan. Yana ɗan shekara uku kacal.

Yayin da ƙananan yatsunsa ke gugan maɓallin roba a rigarsa, wani tsoro mai ƙarfi ya ratsa jikinsa. Bai san dalili ba amma ya san abu ɗaya tabbatacce: bai taɓa son taɓa wa ko ganin maɓalli ba.

Gwagwarmayar zamantakewa

“Kowa ya yi tunanin wani baƙon abu ne na ke yi," James ya shaida wa TRT Afrika yadda mutanen da ke kewaye da shi suke mayar da martani ga ƙin jininsa na wannan abu. "Babu wanda ya fahimci abin da ke faruwa a zuciyata."

A wani lokaci, mahaifin James ya saya masa riga da yake so sosai, sai dai tana da maɓallai. Hakan ya sanya ya ƙi saka ta.

"Mahaifiyata ta roƙe ni da kawai in gwada ta," in ji shi. "Amma ban iya ba. Ganin waɗannan maɓallan ya sa cikina ya yi sanyi."

Yayin da yake girma, James ya koyi ɓoye tsoronsa. Ba kasafai yake magana game da shi ba, yana sane da cewa mutane ba za su fahimta ba.

"Zan ɓoye tsorona kamar laifi," in ji shi.

'Yan'uwansa ma ba su fahimta ba. Su kan yi dariya, su kan yi masa ba'a, su kan kira shi mahaukaci. A ganin su, kawai maɓalli ne. A wajen James kuma, wani abu ne mai ban tsoro da ke sa tsigar jikinsa ​​ta tashi saboda hanyar kallonsa kawai.

Rayuwar kadaici

A makaranta, kayan makaranta na bakanta rayuwar James. Yayin da abokan karatunsa ke sanya riguna masu maɓalli, James ya sami hanyoyin magance matsalar - riguna marasa maɓalli, rigunan T-shirt, duk wani tufafi da ba ya sa shi tsoro.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana irin wannan tsoro a matsayin tsoro mara iyaka da ba a iya juya shi, da wani yanayi ke haifarwa. Suna zama ruwan dare a duk duniya, amma abubuwan da ke haifar da hakan sun bambanta.

Duk da cewa yara na iya nuna alamun farko, kamar yadda yake a yanayin James, yawancin tsoro an san su da bayyana ta hanyar canje-canjen halaye a tsakanin shekaru 15 zuwa 20.

Ya girma a wani ƙaramin gari a Afirka, James ya yi tunanin shi kaɗai ne mutum a duniya da ke da irin wannan matsala mai ban mamaki. Tunanin hakan ya sauya a lokacin da ya shiga makarantar sakandire.

Ya haɗu da sabbin abokansa wanda, a lokacin tattaunawa ta yau da kullun, ya ya fada masa cewa shi ma ba ya jure wa maɓalli.

"Na yi mamaki," in ji James ya fada wa TRT Afrika. "Na daɗe, na yi tunanin ni kaɗai ne."

Tafiyar amincewa

Gano wannan ya canza komai. James ya fara bincike a intanet kuma daga ƙarshe ya sami sunan abin da yake rayuwa da shi.

"Abin farin ciki ne sanin cewa gaskiya ne," in ji shi. "Sanin cewa ba wai kawai ina tunanin hakan ba ne."

Amma har yanzu, bai gaya wa mutane cewa yana jin tsoron maɓallai ba.

"Har yanzu ina ganin mutane ba su fahimci abin da nake ji ba, kuma ko da ambaton sa kawai yana sa ni jin haushi."

Yana guje wa duk wani abu da ke da maɓallai da gangan. Idan ya hadu da shi, sai ya yanke shi ya jefar da shi.

Ba shi kaɗai ba ne ke neman mafita ba tare da wani sabon salo ba. Steve Jobs, wanda ya kafa Apple, yana da ƙyama ga maɓallai, wanda hakan ya bayyana ta hanyar rashin son maɓallan kayan aikin kwamfuta da kuma zaɓin saka riguna nau’in turtleneck.

A wajen James, amsar ita ce sanya rigunan T-shirt da wandon jeans.

A cewar WHO, tunani, motsa jiki salon yoga, motsa jiki na numfasawa, hangen nesa, tunani da kuma motsa gabban jiki a koyaushe duk suna da tasiri wajen sarrafa damuwa da ke tattare da tsoro.

*An sauya sunaye don kare wadanda aka tattauna da su