Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tallafin abinci zai ƙare a Sudan nan da ƙarshen watan Maris sai dai idan an samu sabbin kuɗaɗen tallafi, wanda hakan ke ƙara fargaba ga miliyoyin da mutane da suka faɗa cikin matsalar yunwa mafi girma a duniya.
"A ƙarshen Maris, za mu ƙarar da abincin da muke da shi a Sudan," in ji Ross Smith, Daraktan Shirye-shiryen Gaggawa da Matakan Gaggawa na Shirin Abinci na Duniya, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
"Ba tare da ƙarin kuɗi nan-take ba, miliyoyin mutane za su rasa tallafin abinci mai muhimmanci cikin makonni," in ji shi.
Smith ya ce WFP ta riga ta "tilasta rage abincin da za a ba su don rayuwa".
Gargaɗin ya zo ne bayan kusan shekaru uku na yaƙin basasa a Sudan, inda yaƙi tsakanin sojoji da mayakan RSF ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba mutane miliyan 11 da matsugunansu.
Matsanancin ƙarancin abinci
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, fiye da mutane miliyan 21 -- kusan rabin al'ummar Sudan -- yanzu suna fuskantar matsalar ƙarancin abinci.
Wani bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ya tabbatar da cewa yunwa ta ɓarke a El Fasher, babban birnin Arewacin Darfur, wanda dakarun RSF suka mamaye a watan Oktoba.
An kuma tabbatar da cewa yunwa ta ɓulla a Kadugli, da ke maƙotaka da Kordofan, wanda yanzu yake taka rawa a rikicin ƙasar.











