Sojojin Sudan sun daƙile wani babban hari da ‘yan tawayen (RSF) da abokiyarta, Sudan People’s Liberation Movement–North (SLPM-N), suka kai wa garin Al-Kuweik a Kudancin Kordofan, in ji majiyoyin soji.
Da yake magana da Anadolu a ranar Laraba, majiyoyin sun ce rundunonin soji sun yi fito na fito da harin tun da wuri a safiyar, wanda ya yi nufin jawo asarar rayuka da kayan aiki kuma suka tilasta wa maharan janyewa.
Sun kara da cewa dakarun gwamnati sun kwace motoci masu sulke da na yaki a lokacin fafatawar.
Babu wani martani nan take daga RSF ko SPLM-North kan rahoton.
Bidiyoyi da sojoji suka yada a kafafen sada zumunta sun nuna murnar da aka dinga yi bayan an daƙile harin.
A 'yan makonnin da suka gabata, jihohin Kordofan guda uku na Sudan — Arewa, Yamma da Kudu — sun sha fama da munanan rikice-rikice tsakanin sojoji da RSF, wanda ya tilasta dubban fararen hula barin gidajensu.
Daga cikin jihohin Sudan 18, RSF na da iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur a yamma, sai dai wasu sassan arewacin North Darfur da ke ci gaba da kasancewa karkashin ikon sojoji.
A gefe guda, sojoji suna rike da mafi yawan wurare na sauran jihohi 13 a kudu, arewa, gabas da tsakiyar kasar, ciki har da babban birnin Khartoum.
Rikicin tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda ya fara a watan Afrilu 2023, ya yi sanadin kashe dubban mutane kuma ya tilasta miliyoyin mutane barin gidajensu.







