Dan Iraki mai zayyana ya kammala rubuta Kur'ani mafi girma da hannu a Istanbul
Dan Iraki mai zayyana ya kammala rubuta Kur'ani mafi girma da hannu a Istanbul
Ali Zaman yana fatan cewa, rubutun zayyanar, wanda ya dauke shi shekaru shida kafin ya kammala, zai kasance a Turkiya, yana nuna al'adar tarihin kaligirafi a kasar.
13 awanni baya

Wani gwanin kera gwal daga kasar Iraki ya shafe shekaru shida yana rubuta abin da ake ganin shi ne Al-Kur'ani mai tsarki mafi girma da aka taba rubutawa da hannu a duniya, a birnin Istanbul. Wannan rubutun yana da shafuka masu tsawon mita hudu da fadin mita 1.5.

Ali Zaman, wanda aka haifa a shekarar 1971 a Sulaymaniyah, Iraki, ya fara sha'awar rubutun zayyana na Musulunci tun yana karami.

Bayan ya bar sana'arsa ta kera gwal a shekarar 2013, ya mayar da hankali kacokan kan wannan fasaha.

A shekarar 2017, Zaman ya koma tare da iyalinsa zuwa unguwar Fatih a birnin Istanbul domin ci gaba da aikinsa.

Wannan babban Al-Qur'ani, wanda ya dauki shekaru shida ana rubutawa, an rubuta shi gaba daya da hannu ta amfani da alkaluman gargajiya na itace a cikin rubutun thuluth, wanda wani nau'in kaligrafi ne na Larabci.

Kowane shafi, idan aka bude, yana da fadin mita uku. Zaman ya guji amfani da kayan zamani, yana rubuta kowane harafi da kansa cikin kulawa. A cikin karamin daki a cikin ginin masallacin Mihrimah Sultan a Istanbul, ya shafe kowace rana yana aiki kan wannan rubutu, ya kan dakata ne kawai don cin abinci da sallah.

Zaman ya dauki nauyin aikin gaba daya da kansa, duk da matsalolin lafiyar da suka tilasta masa dakatarwa a shekarar 2023.

Ya lashe lambobin yabo na kasa da kasa da dama, ciki har da na farko a rubutun thuluth da naskh a kasashen Syria, Malaysia, Iraki, da Turkiyya.

Ya samu izini (ijazah) daga manyan malamai a fannin kaligrafi kuma ya karbi mafi kololuwar lambar yabo ta “Distinction” a shekarar 2017 a gasar Hilye-i Serif ta kasa da kasa a Turkiyya daga Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan.

Da yake magana game da aikin ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Zaman ya ce: “Abin farin ciki ne a kirkiri wani abu da mutane kadan ne za su iya yi ko ma su yi kokarin yi. Kowane harafi yana nuna ruhin da kokarin da aka saka a cikin wannan aiki.”

Danshi, Rekar Zaman, ya bayyana cewa iyalinsu sun koma Turkiyya saboda kasar tana daraja kaligrafi da fasahar Musulunci fiye da Iraki.

Ya kara da cewa samun kayan aiki masu dacewa yayin annobar COVID-19 ya kasance kalubale, amma sun ci gaba da jajircewa.

Al-Kur'anin da aka kammala ya zarce girman rubutun da aka sani a baya, wanda ya kasance da tsawon mita 2.28 da fadin mita 1.55.

Iyalin suna shirin adana wannan rubutu cikin kulawa kuma suna fatan zai ci gaba da kasancewa a Turkiyya, yana nuna tarihin kasar na kaligrafi.