Shugaban hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) Patrice Motsepe ranar Asabar ya ce daga shekarar 2028 za a riƙa gudanar da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka bayan shekara huɗu-huɗu.
Motsepe ya ce hakan wani ɓangare ne na gagarumin sauyin da suke burin kawowa a fagen ƙwallon ƙafar Afirka domin ya dace da jadawalin ƙasashen duniya.
Gudanar da gasar AFCON bayan shekaru biyu-biyu yana samar wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Afirka kuɗin shiga, amma Motsepe ya ce ƙaddamar da gasar lig ta ƙasashen Afirka - wadda take kama da gasar UEFA - za ta taimaka wajen sama wa ƙasashen kuɗin shiga.
"Babban abin da ke gabanmu a yanzu shi ne gasar AFCON amma daga shekarar 2027 za mu je Tanzania, Kenya da Uganda, kuma gasar AFCON ita ce wadda za a yi a 2028," a cewar Motsepe a hira da manema labarai a birnin Rabat na ƙasar Maroko, a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin ƙasashen Afirka, wato AFCON 2025.
Damar ɗaukar nauyin gasar
Ya ƙara da cewa za a bayar da damar ɗaukar nauyin gasar ga ƙasashen da ke sha’awar karɓar baƙuncin Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka ta 2028.
"Bayan Gasar Duniya ta FIFA ta Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa a 2029 za mu gudanar da gasar farko ta lig ta ƙasashen Afirka ... inda za a saka ƙarin kuɗaɗe da kayan aiki da fafatawa a gasar.
"A wani ɓangare na shirin yin gasar, za a riƙa gudanar da gasar AFCON bayan shekara huɗu-huɗu."
















