| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe mutum tara a Afirka ta Kudu
'Yansanda suna gudanar da bincike game da harin da 'yanbindiga suka kai a garin Bekkersdal na ƙasar Afirka ta Kudu inda suka kashe mutum tara datre da jikkata aƙalla mutum goma.
'Yanbindiga sun kashe mutum tara a Afirka ta Kudu
'Yansandan Afirka sun soma bincike domin gano musabbabin kai harin / Reuters
21 Disamba 2025

Wasu ‘yanbindiga sun buɗe wuta a wani gidan sayar da barasa da ke wajen birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu ranar Lahadi inda suka kashe mutum tara, a cewar ‘yansandan ƙasar.

Wannan shi ne karo na biyu da irin wannan lamari ke faruwa a ƙasar a cikin wata ɗaya.

Mutum aƙalla goma sun jikkata yayin da ‘yanbindigar suka kai hari a gidan sayar da barasar a garin Bekkersdal, a yankin da ake haƙar zinari mai nisan kilomita 40, kudu maso yammacin babban birnin ƙasar.

Tun da farko ‘yansanda sun ce mutum goma ne suka mutu amma daga bisani suka ce mutum tara aka kashe.

Maharan da ke cikin ababen hawa biyu "sun buɗe wuta kan masu sayar da barasar sannan suka ci gaba da ɓarin wuta a gidan barasar kafin su tsere," a cewar wata sanarwa da rundunar ‘yansanda ta fitar.

Cikin waɗanda aka kashe har da wani direban motar haya, a cewar Kwamishinan ‘yansanda Manjo Janar Fred Kekana a hirarsa da gidan talbijin na SABC.

Tuni dai aka ƙaddamar da neman maharan ruwa-a-jallo, in ji rundunar ‘yansandan ƙasar.

MAJIYA:AFP