A wasansu na buɗe Gasar Kofin Afirka na AFCON 2025, ƙasashen Zambia da Mali sun yi canjaras da ci 1-1 ranar Litinin.
Ɗan wasan Zambi mai taka leda a Leicester City ta Ingila, Patson Daka shi ne ya ci ƙwallon ana dab da tashi daga wasan, wanda ta bai wa Zambia damar raba maki da Mali.
A can Leicester, sau ɗaya kacal Daka ya taɓa cin ƙwallo a gasar Championship ta Ingila a wannan kakar.
Daka ya yi ta-maza ya jefa kansa don karɓar ƙwallon da Mathews Banda ya auno a minti na biyu na ƙarin lokaci a ƙarshen wasan, inda ya ci ƙwallon da ta bai wa tawagar mai laƙabin Chipolopolo maki guda.
Mali ta fi rinjaye a yawancin wasan na ƙasashen Rukuni A, duk da cewa El Bilal Toure ya kasa cin bugun ɗurmen da aka ba shi a ƙarshen rabin farko na wasan da aka buga a Stade Mohammed V a Casablanca.
Golan Zambia, Willard Mwanza ne ya tare bugun na Toure.
Farkewar da Zambia ta yi wadda ta janyo suka raba maki ɗai-ɗai ya yi wa Maroko daɗi, sabod ta ci wasanta da Komoros, wanda ya ba ta maki uku, da ke nufin yanzu tana saman teburin Rukunin A.
Ranar Lahadi Maroko za ta kara da Mali a birnin Rabat, a ranar da ita ma Zambia za ta kece raini da Comoros a cigaba da gasar ta AFCON 2025.


















