| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Abokan hamayya sun yi iƙirarin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na Guinea-Bissau
Hukumar zabe da masu sa ido sun gargaɗi masu zabe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da masu tattara sakamako game da sanar da kowane irin sakamako.
Abokan hamayya sun yi iƙirarin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na Guinea-Bissau
'Yan ƙasa sun kaɗa kuri'a ranar Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa, ana sa ran sakamakon zai fito zuwa ranar Alhamis.
25 Nuwamba 2025

Shugaban ƙasa mai ci Umaro Sissoco Embalo da ɗan takara mai zaman kansa Fernando Dias dukkansu sun yi iƙirarin nasara a zaben shugaban kasa na Gini-Bisau da aka gudanar a karshen makon jiya, yayin da kasar ke jiran sakamako.

Dias, wanda ake masa kallon babban mai fafatawa a zaben, ya taya masu kada kuri'a murna bisa fitowa domin yin zabe, inda a ranar Litinin ya ce hakan alama ce ta muradin sauyi, a cewar jaridar yanar gizo mai zaman kanta O Democrata GB.

"Muna da bayananmu kuma mun san mene ne sakamakon. An ci wannan zaben ne a zagaye na farko. Muna jiran kawai hukumar da ta dace (hukumar zabe) ta tabbatar," a cewar rahoton.

'Yan takara goma sha biyu suka fafata a neman kujerar shugaban ƙasar.

"Ba za a je zagaye na biyu ba"

A gefe guda, Oscar Barbosa, mai magana da yawun yakin neman zaben Embalo, ya shaida wa manema labarai a babban birnin Bissau cewa dan takararsu ya ci kuma "ba za a je zagaye na biyu ba."

Hukumar zabe ta yi alkawarin bayyana sakamakon karshe na zaben nan da zuwa ranar Alhamis.

Ta gargaɗi masu zabe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da masu tattara sakamako game da sanar da kowane irin sakamako.

Dan takarar mai zaman kansa ya ce ya samu rinjaye a kusan dukkan yankuna. Tun da faro kuma, ya yi tir da yiwuwar yunkurin tsoma baki a yayin kirga kuri'u.

Dias na da goyon bayan tsohon Firaminista Domingos Simoes Pereira, wanda shi ne babban wanda ya fafata da Embalo a zagaye na biyu a 2019.

An hanay mai hamayya yin takara

An hana Pereira, na Jam'iyyar African Party for the Independence of Guinea and Cape Verde (PAIGC), wadda ta jagoranci yunƙurin neman 'yanci daga Portugal a 1974, shiga zaben wannan shekarar bayan hukumomi sun ce ya shigar da takardunsa a makare.

Kimanin rabin mutanen kasar ta na Gini-Bisau miliyan 2.2 sun cancanci kada kuri'a a zabukan.

An kiyasta cewa fitar masu zabe ya wuce kashi 65%.

A ranar Litinin, wani ƙawancen masu sa ido kan zabe, ciki har da na Tarayyar Afirka, sun yi kira ga dukkan bangarori da su jira sanarwar hukuma kafin fitar da sakamako.

Shugaban masu sa ido na Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Gini-Bisau a zabukan na 23 ga Nuwamba, jakadan Ghana Baba Kamara, ya ce tsarin zabe ya tafi dai-dai.

Masu sa ido na kasa da kasa

Fiye da masu sa ido 200 na kasa da kasa sun kasance a kasar don duba tsarin zaben, ciki har da daga ECOWAS, Tarayyar Afirka da kuma Ƙungiyar Ƙasashen da ke Magana da Turancin Portugal.

Tun daga lokacin da ya hau kujerar mulki a 2020, an samu rahotanni da dama na yunkurin kifar da gwamnatin Embalo, abin da ke nuna zurfin hamayyar da ya ke fuskanta.