Shugabannin ƙasashe da wakilan shugabannin ƙasashen Afirka sun bi sahun dubban masu jimami a wajen taron jana'izar tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga a ranar Juma'a, ɗan rajin kare dimokuraɗiyya da kawo sauyi, wanda ya rasu a makon nan a India yana da shekaru 80 a duniya.
Al'ummar Kenya sun yi fitar farin ɗango domin nuna alhininsu ga Odinga tun bayan rasuwarsa ranar Laraba, lamarin da ke nuni da irin tasirin da ɗan siyasar da ake girmamawa ke da shi kan harkokin siyasa a ƙasar da ke gabashin Afirka.
Dubban mutane ne suka cika filin wasan ƙwallon kafa inda aka lulluɓe akwatin gawar Odinga da tutar kasar domin yi masa jana’iza ƙarƙashin Cocin Anglican a Nairobi babban birnin Kenya. Mutanen sun yi ta rera waƙen yabo tare da daga hotunan Odinga, yayin da wasu ke ɗauke da rassan bishiya, alamar zaman lafiya da haɗin kai a al'adar Kenya.
An tsaurara matakan tsaro a filin wasan bayan da mutane uku suka mutu a yayin turmutsutsun da ya afku a inda jama’a ke kallon gawar a filayen wasa daban-daban.
Odinga ya yi takarar shugabancin Kenya sau biyar a cikin sama da shekaru talatin, kuma duk da bai taɓa samun nasarar zama shugaban ƙasa ba, ana mutunta shi saboda fafutukar da ta taimaka wa Kenya wajen zama kasar ɗabbaka dimokuraɗiyya.
An fara kai gawar Odinga majalisar dokokin kasar da safiyar Juma'a kafin jana'izar, wanda hakan girmamawa ce da aka keɓe ga shugaban ƙasa da tsoffin shugabannin ƙasar.
Shugaba William Ruto ya ce Odinga ya cancanci karramawa saboda kasancewar sa ɗan majalisa na tsawon shekaru 15, rawar da ya taka na da muhimmanci wajen tsara wasu dokoki masu tasiri a tarihin Jamhuriyar Kenya.
Ruto ya yi wa Odinga yaƙin neman zaɓe a shekarar 2007 - zaɓen da aka yi ta taƙaddama da shi wanda ya kawo tashe-tashen hankula. Mutanen biyu sun kasance abokan hamayya a zaɓukan da suka biyo baya, ciki har da na baya-bayan nan a shekarar 2022.
Shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a bana, bayan shafe watanni ana zanga-zangar adawa da gwamnati, kuma yarjejeniyar ta sanya ‘yan jam’iyyar adawa sun samu muƙaman ministoci.
Daga cikin wadanda suka yi makokin har da matar Odinga Ida, da ‘ya’yanta Winnie da Rosemary, da kuma ɗanta Raila Odinga Junior.
Winnie, wadda ke tare da shi a India, ta jagoranci masu makoki waje rera waƙa a cikin yaren Luo na ƙasar. Ta ce mijinta ya mutu yana da "ƙarfi, da mutunci da kuma alfahari" bayan ya fita tattakin safe da ya saba yi yana zagaya asibitin sau biyar haka.
Ɗansa Junior, ya ce zai kula da iyalinsa a matsayin ɗan da aka bari.
Shugaba Ruto ya jagoranci masu zaman makoki wajen rera waƙar da Odinga ya fi so, wato "Jamaica Farewell" ta Harry Belafonte, ya kuma ce ya taimaka masa ya ci gaba da riƙe ƙasar a farkon shekarar nan.
“A duk lokacin da al’umma ke buƙatarsa yana ajiye ko shi waye ya taimaka musu ba ƙaƙƙautawa,” inji Ruto.