Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Ministan Tsaro Yasar Guler, da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri Ibrahim Kalin sun gana a ranar Lahadi a Ankara tare da takwarorinsu na Syria don tattaunawa a matakin ƙoli.
A cewar majiyoyin diflomasiyya, Fidan, Guler, da Kalin sun tattaunawa tare da Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad Hassan al Shaibani da Ministan Tsaro Murhaf Abu Qasra, da Shugaban Hukumar Leken Asiri Hussein Salameh a ranar Lahadi.
Taron ya mayar da hankali kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Turkiyya da Syria, da kuma ci gaban da aka samu kwanan nan.
A ranar Asabar, Ministan Tsaron Syria Murhaf Abu Qasra ya gana da Shugaban Hukumar Masana'antar Tsaro ta Turkiyya Haluk Gorgun tare da tawagarsa a birnin Dimashƙu.
A cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Tsaron Syria da aka wallafa ta tashar Telegram dinta, ɓangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa daban-daban na moriyar juna kuma sun bincika hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro.