Hukumar Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare ɗan jaridar Birtaniya mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa gwamnatin Isra’ila a yayin wani rangadin gabatar da jawabai da ya yi a Amurka.
Hamdi ya gabatar da jawabi a wani babban taro na Majalisar Hulɗa da Musulunci ta Amurka a birnin Sacramento na Jihar California a ranar Asabar kana an shirya zai gabatar da wani jawabi a ranar Lahadi a ɗaya daga cikin tarukan ƙungiyar a Florida.
A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar CAIR ta ce an tsare Hamdi ne a filin jirgi sama na San Franscisco.
Hamdi ya bayyana a matsayin mai sharhi kuma mai jawabi a wani shirin talabijin na Birtaniya. A ranar Lahadi ƙungiyar CAIR ta yi kira da a sake shi kuma ta zargi gwamnatin Trump da tsare shi saboda sukar da yake yi wa gwamnatin Isra'ila.
"Muna sanar da cewa ba a kori Mista Hamdi ba amma yana nan a tsare. Lauyoyinmu da abokan hulɗarmu suna aiki don kawo ƙarshen wannan rashin adalci," kamar yadda Majalisar Hulɗa da Musulunci ta Amurka (CAIR) ta wallafa a shafinta na X.
Kama wani ɗan ƙasar Birtaniya da ya ziyarci Amurka saboda yin magana game da kisan ƙare-dangi da ake zargin wata ƙasa da aikatawa shi ne "cin zarafi na 'yancin faɗar albarkacin baki na baya bayan nan da gwamnatinmu ta yi," in ji CAIR.
"Dole ne Amurka ta daina tsare masu sukar Isra'ila a ƙarƙashin matsin lamba daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke goyon bayan Isra'ila; irin waɗannan ayyukan suna fifita muradun Isra'ila fiye da na Amurka kuma dole ne a kawo ƙarshensu," in ji sanarwar.
Tun daga watan Janairun shekaran nan, gwamnatin Trump take ci gaba da tsaurara matakan shige da fice, ciki har da ƙara tantance shafukan sada zumunta, da soke biza ga mutanen da ta yi iƙirarin sun nuna farin ciki bisa kisan mai ra'ayin riƙau Charlie Kirk, da kuma korar masu riƙe da bizar ɗalibai da masu shaidar katin zama ɗan ƙasa waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga Falasɗinawa kuma suka soki hare-haren Isra'ila a Gaza.














