UNGA 80: Ɓaramɓarama bakwai da Trump ya yi a taron MDD na New York
DUNIYA
4 minti karatu
UNGA 80: Ɓaramɓarama bakwai da Trump ya yi a taron MDD na New YorkShugaban Amurka ya yi ɓaramɓarama, da cika baki da kushe wasu a taron Majalisar Dinkin Duniya - daga kan maganarsa a kan na'urar teleprompter da ake karanto jawabi a cikinta har zuwa sauran abubuwan ban dariya da ya yi.
Trump a Majalisar Dinkin Duniya ran Talata.
23 Satumba 2025

Majalisar Dinkin Duniya —

An shirya zauren taron Majalisar Dinkin Duniya tsaf don gabatar da taron.

UNGA a shekara 80. An jere tutocin ƙasashe a cikin zauren mai adon marmara, masu fassara sun zauna tsaf, jakadun kasashe da jami’an diflomasiyya sun mai da hankali sosai, kafofin watsa labarai na duniya suna nan da alkaluman rubutunsu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya hau dandamali da safe a ranar Talata. Mutumin da ya taba mamaye komai wajen mayar da wannan zaure zuwa nasa a shekarar 2018, a bana Trump ya sake yin abin da ya saba.

An ɓarke da dariya a ɓangarori daban-daban na cikin zauren. Wasu dariyar Allah da Annabi, wasu kuma ta shegantaka, wasu kuma ta jin kunya.

Ga manyan abubuwa bakwai da suka fi ɗaukar hankali.

1. Matsalar na'urar karanto jawabi

Trump ya fara da cewa ana masa zagon ƙasa. “Na’urar karatu ba ta aiki,” ya sanar. “Amma ba matsala. Zan yi magana daga zuciyata.” Sai ya kara da cewa: “Duk wanda ke da alhakin kula da wannan abu yana cikin matsala babba.” An ɓarke da dariya a cikin zauren. Hankula sun fara kwanciya.

2. Matsalar na’urar hawa sama ‘escalator’

Yana tsaka da jawabi, sai Shugaban Amurka ya karkata. “Abin da kawai na samu daga Majalisar Dinkin Duniya shi ne tsayawar na’urar hawa sama ta escalator ina tsaka da tafiya” ya ce. “Da ba don cewa Uwargidan Shugaba tana cikin koshin lafiya ba, da ta fadi. Amma tana cikin koshin lafiya. Ni ma haka.”

Dariya ta ɓarke a tsakanin wakilan, matsalar yau da kullum ta zama abin nishadi.

3. Kalamai masu tsauri

Trump ya yi wa Majalisar Dinkin Duniya shaguɓe da dariya. “Mene ne aikin Majalisar Dinkin Duniya? Abin da suke yi kawai shi ne rubuta wasika mai tsauri.” Wata irin dariya ta ɓarke a cikin zauren, yayin da wasu kuma suka yi shiru.

4. Kyautar da bai so

Shugaban Amurka ya yi ikirarin kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe bakwai cikin watanni bakwai. “Kowa yana cewa ya kamata in samu Kyautar Zaman Lafiya ta Nobel,” ya ce. “Amma ban damu da kyaututtuka ba, abin da na damu da shi shi ne ceton rayuka.”

Aka yi dariya a zauren, ba don yadda ya nuna kautar ba ta dame shi ba sai don yadda ya yabi kansa a cikin kalaman.

5. Hular Trump

Sai ya kawo wani abu. “Ina da hula. Ta ce, ‘Trump yana da gaskiya a kan komai.’”

A wannan wurin na diflomasiyya, wani abu kamar talla. Ba a wurin da ya dace ba, amma abin a yi dariya don hakan.

6. Na kware sosai a wannan abu

Shugaban Amurka ya karkata. “Na kware sosai a wannan abu. Kasashenku suna tshiga uku.”

Kalaman da aka nufa ga Ƙasashen Yamma sun yi tasiri sosai. Zauren ya sake ɓarkewa da dariya, wasu saboda mamaki, wasu kuma saboda shi kadai zai iya fadin hakan.

7. Mahogany, marmara, da ciniki

Trump ya koma kan wani batu da ya saba fada, yana gaya wa taron cewa ya taba bayar da shawarar sake gyara hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya a New York — bene mai marmara, da launin mahogany, duk abin da ya dace da dala miliyan 500.

Wata sata, ya ce, idan aka kwatanta da kudin da aka kashe don gyaran da bai kai wannan ba. Kalaman sun zama kamar talla da kuma barkwanci, suna nuna ginin Majalisar Dinkin Duniya a matsayin alamar almubazzaranci.

Daga baya a cikin jawabinsa na tsawon awa guda, Trump ya yaba da “kwal mai tsabta, mai kyau.” Kalaman sun yi kama da ba su dace ba a cikin zauren da batun sauyin yanayi ya mamaye ajandarsa. Dariya ta sake barkewa, tana dauke da wani irin yanayi na ban dariya.

Jawabin Trump ya yi ta kaiwa tsakanin barkwanci da suka, yabo da kuma tsokana. Gaza, Siriya, amincewa da Falasdinu, Ukraine, hijira — wasu batutuwa masu mahimmanci sun shiga ciki, amma a tsakanin su, akwai irin salon Trump na musamman.

A wannan Talatar, Trump, wanda yake wakiltar New York, ya juya wannan taron duniya ya zama kamar taron jama’ar birnin New York: suna dariya, suna jin rashin tabbas, amma suna jin nishadi.

Rumbun Labarai
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Ga manyan batutuwa huɗu daga jawabin Sarkin Qatar a taron UNGA
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000
Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa