Lionel Messi ya miƙa saƙon jaje ga tawagar Argentina ta ‘yan-ƙasa da shekaru 20, bayan Morocco ta doke su da ci 2-0 a gasar da aka kammala ranar Lahadi a Chile.
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, inda ita kuma Argentina ta yi rashin nasara a gasar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi.
Messi ya wallafa a Instagram cewa, “Ku saurara, yara!!!! Kun taka rawar gani a gasar, kuma duk da cewa dukkanmu mun so ganin kun ɗaga kofin, mun yi murna da abin da kuka ba mu da kuma alfaharin yadda kuka kare tutar ƙasarmu da zuciyarku.”
Tawagar matasan Argentinan ta yi fatan lashe kofin a bana, don ƙasar ta zama tana riƙe da babban kofin duniya da kuma na matasa ‘yan ƙasa da shekaru 20 a lokaci guda.
Wannan rashin nasara ta ja hankalin tauraron ɗan wasa, Lionel Messi, wanda ya taɓa lashe gasar ta U20 tare da Argentina a shekarar 2005.
Argentina ta yi ƙoƙari
Tawagar Argentina ta yi rawar gani a gasar, inda ta zura ƙwallaye 15 kuma aka ci ta ƙwallo 4 kacal.
Masu sharhi da dama sun yi tunanin Argentina ce za ta ɗaga kofin na bana, sakamakon tarihin nasarar da ta yi a gasar a shekarun baya.
Sai dai ita ma Morocco ta nuna bajinta, inda ta zamo ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga kofin, bayan Ghana a shekarar 2009.
Duk da cewa wannan ne karo na huɗu da Morocco ta je gasar, nasarar ta ba ta damar zamowa ƙasa ta 14 da ta ɗaga kofin a tarihi.