A lokacin da Mwanaisha Juma, wata mata mai shekaru 34 da haihuwa, kuma uwa ga yara biyu a ƙasar Tanzania, ta fara lura da alamun fara balaga da wuri ga 'yarta mai shekaru bakwai, ta shiga ruɗani.
“Na yi tunanin cewa wataƙila abu ne da ke faruwa a wasu iyalai kawai,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika a lokacin da take zaune a ƙaramin gidanta da ke birnin Dar es Salaam.
“Amma lokacin da na tattauna da wasu iyaye mata da ke zaune a ginin da nake ciki, sai na gano wasu yara uku da ke fuskantar irin wannan matsala.”
Abin da Mwanaisha ba ta sani ba shi ne, kwalaben roba da iyalinta ke amfani da su wajen shan ruwa a kullum, kayan wasan yara masu arha da 'ya'yanta ke amfani da su, da kuma kayan kwalliyar da take shafawa a jikinta kowace safiya, duk suna iya ƙunsar sinadarai da ke kawo cikas ga tsarin sinadaran hormones da ke kula da daidaiton ayyukan jiki.
Labarin Mwanaisha ba wani abu ne da ya faru da ita ita kaɗai ba.
Suna fuskantar sinadarai masu illa ga lafiya ba tare da sanin hakan ba
A faɗin nahiyar Afirka, iyalai na fuskantar haɗarin sinadarai masu kawo cikas ga tsarin hormones na jiki (Endocrine-Disrupting Chemicals – EDCs) ba tare da sun sani ba, ta hanyar kayayyakin da suke amfani da su a kullum. Kayayyakin sun haɗa da mazuban abinci, kayan girki, kayan kwalliya, kayan wasan yara da kuma tufafi.
Wani sabon rahoto da Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka fitar a ranar 17 ga Nuwamba, ya yi gargaɗin cewa waɗannan sinadarai na iya haifar da mummunar illa ga lafiyar ɗan Adam da muhalli fiye da yadda aka fahimta a baya.
A can nesa da Afirka ta Gabas, a birnin Kisumu na ƙasar Kenya, wani manomi mai shekaru 42 mai suna Joseph Otieno, ya ce ya lura da wasu sauye-sauye masu tayar da hankali a cikin al'ummarsa.
“Cikin shekaru goma da suka gabata, na lura cewa matasa maza da dama a ƙauyenmu na fuskantar matsalolin haihuwa,” in ji shi yayin da yake tsaye kusa da ƙaramar gonarsa da ke wajen birnin.
“Har ila yau, tafkin da muke kamun kifi ya sauya. Wasu nau'ikan kifaye sun fara ɓacewa, yayin da waɗanda muke kama wa ba su zama kamar da ba.”
Abubuwan da Joseph ya lura da su sun yi daidai da wasu sakamakon binciken kimiyya da ke danganta fuskantar waɗannan sinadarai da matsalolin haihuwa, matsalolin bunƙasar jiki da kuma lalacewar muhalli da halittun da ke cikinsa.
Rahoton na UNEP da WHO, mai taken “Matsayin Binciken Kimiyya Kan Sinadaran da Ke Kawo Cikas ga Tsarin Hormones na Jiki na Shekarar 2026”, ya yi amfani da sakamakon binciken kimiyya da aka gudanar tsawon sama da shekaru goma.
Sinadaran da ke kawo cikas ga tsarin hormones na jiki su ne wasu sinadarai da ke shafar tsarin ƙwayoyin gland da hormones, waɗanda ke kula da muhimman ayyukan jiki kamar girma, bunƙasa, haihuwa da kuma narkar da abinci.
Waɗannan sinadarai na iya shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci, ruwan sha, iska, ƙura da kuma taɓa kayayyakin amfanin yau da kullum kai tsaye.
“Bayanai sun nuna cewa waɗannan sinadarai suna cikin kayayyakin da mutane ke amfani da su a kullum,” in ji Sheila Aggarwal-Khan, Daraktar Sashen Masana'antu da Tattalin Arziki na Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP).
Ta ce, “A yanzu muna da sabbin hujjoji na binciken kimiyya da aka tattara tsawon sama da shekaru goma, waɗanda ke nuna yadda waɗannan sinadarai za su iya cutar da mutane da muhalli.
“Saboda haka, samar da tsare-tsare da dokoki da za su tabbatar da cewa kayayyakin da ba su da illa ga lafiya ne kawai ke isa hannun masu amfani, yana da matuƙar muhimmanci wajen kare mutane, namun daji da kuma tsarin halittu da ke cikin muhalli.”
Lamarin ya fi illata yara
Daga cikin fitattun sinadarai masu kawo cikas ga tsarin hormones na jiki (EDCs), akwai ‘bisphenols’ da ‘phthalates’, waɗanda ake samu a wasu nau’ikan robobi da kayan wasan yara; sinadaran ‘per- and polyfluoroalkyl substances’ (PFAS), waɗanda ake amfani da su wajen kera kayan haɗa abinci da yadudduka; da kuma ‘parabens’, waɗanda ake amfani da su a kayayyakin kula da jiki.
Bincike ya danganta mu’amala da waɗannan sinadarai da raguwar ingancin maniyyin namiji, matsalolin haihuwa da suka haɗa da cutar ‘endometriosis da polycystic ovary syndrome’, kiba, ciwon suga na nau’i na biyu, da kuma wasu nau’ikan cutar daji da ke da alaƙa da kwayoyin halitta.
Aggarwal-Khan ta ce, “Yara sun fi fuskantar haɗari,” saboda hormones na taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da girma, bunƙasar kwakwalwa da kuma balaga.
Haka kuma, yara na iya shiga mu’amala da waɗannan sinadarai fiye da manya idan aka kwatanta da nauyin jikinsu, saboda suna cin abinci, shan ruwa da shakar iska fiye da manya idan aka yi la’akari da nauyin jikinsu.
Illolin tattalin arzikin da waɗannan sinadarai ke haifarwa na da matuƙar girma. A duk shekara, mu’amala da EDCs na janyo asarar kuɗi sama da dala tiriliyan 1.1 ga tattalin arzikin duniya, sakamakon kuɗaɗen kula da lafiya da kuma raguwar ingancin ayyukan yi. Sai dai Aggarwal-Khan ta yi gargaɗin cewa mai yiwuwa wannan adadi bai nuna cikakken girman matsalar ba.
Ta ce, “An yi rajistar sinadarai da gaurayen sinadarai sama da 350,000 domin amfani da su a faɗin duniya, amma kaɗan ne kawai aka gudanar da bincike a kansu domin tantance yiwuwar tasirinsu wajen kawo cikas ga hormones. Wataƙila abin da muke gani yanzu kaɗan ne kawai daga cikin babbar matsalar da ke ɓoye.”
Dangane da namun daji kuwa, masana kimiyya sun gano sauye-sauye a tsakanin yawan jinsin dabbobi maza da mata, raguwar nasarar hayayyafa, da kuma sauye-sauye a halayen neman abokin saduwa, ƙaura, neman abinci da kuma kauce wa mafarauta.
Wasu daga cikin waɗannan sinadarai na iya yin tafiyar dubban kilomita, har su isa ga namun dajin yankin Arctic, duk da cewa wuraren da ake samar da su ko gonakin da ake amfani da su suna da nisa sosai.
Amincin kayayyaki
Rahoton ya buƙaci a inganta sa ido kan muhalli, a tsaurara gwaje-gwajen kayayyaki, a samar da ƙa’ida guda ɗaya ta tantance sinadaran da ke kawo cikas ga tsarin hormones na jiki, tare da ƙara bayyana bayanai kan yadda ake amfani da su.
Aggarwal-Khan ta ce, “Kamfanoni na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa ba su da illa ga masu amfani da su. Maimakon jiran sabbin dokoki ko yiwuwar fuskantar hukunci kan illolin kayayyaki, kamfanoni za su iya ɗaukar mataki tun da wuri, ta hanyar tantance kayayyakin da suke samarwa da gudanar da gwaje-gwaje domin gano haɗurra da kuma magance su tun kafin su ƙara ta’azzara.”
Akwai wasu hanyoyin da suka fi aminci, waɗanda za a iya amfani da su a madadin waɗannan sinadarai. Misali, ana iya amfani da gilashi, bakin ƙarfe da ƙarfen siminti wajen ƙera kayan girki da na adana abinci; wasu sinadarai masu adana kayan kwalliya da ba su da illa; da kuma yadudduka da ba a yi musu amfani da sinadaran PFAS ba.
Masu sayayya ma za su iya ɗaukar matakai domin kare kansu, ta hanyar zaɓar madaukin gilashi ko bakin ƙarfe, neman kayayyakin da ke bayyana sinadaran da aka yi amfani da su wajen ƙera su, da kuma buɗe tagogi domin samun iska mai kyau a gidajensu akai-akai.
Sai dai Aggarwal-Khan ta jaddada cewa matakan da mutum zai ɗauka shi kaɗai ba za su wadatar ba.
Ta ce, “Zaɓin da mutum ya yi shi kaɗai ba zai iya kawar da haɗuwarvsa da waɗannan sinadarai gaba ɗaya ba. Duk da cewa sauya wasu halaye na iya taimakawa, wajibi ne a magance tushen matsalar ta hanyar kafa dokoki.”
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Joseph Otieno na ci gaba da kasancewa mai kyakkyawan fata.
Ya ce, “Muna buƙatar kare yaranmu da kuma ƙasarmu. Idan gwamnatoci da kamfanoni suka haɗa kai, na yi imanin za mu iya inganta al’amura domin al’ummomin da za su zo nan gaba.”












