Kasuwannin kuɗaɗe da hannayen-jari na Nijeriya sun fara watan Nuwamban shekarar 2025 da ƙafar hagu inda ƙimar kuɗin ƙasar Naira da hannayen-jari suka faɗi bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar yiwuwar kai harin soji Nijeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.
Alƙaluma daga Babban Bankin Nijeriya sun nuna cewa naira, wadda aka sayar 1,421 ga kowace dalar Amurka ta koma 1,436 ga dalar Amurka ranar Litinin inda darajarta ta faɗi da kashi 1.03 cikin 100 ko kuma da naira 14.61 a yini ɗaya, kamar yadda jaridar Punch ta Nijeriya ta ruwaito.
Kazalika darajar kuɗin ta faɗi a kasuwar bayan fage zuwa N1,455 ga dalar Amurka, lamarin da ya nuna ƙarin fargabar masu zuba jari da kuma matsin neman kuɗaɗen waje.
Faɗuwar ƙimar kuɗin ta biyo bayan zargin da Trump ya yi a wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa aka yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar, inda ya ayyana Nijeriya matsayin wata ƙasa wadda ke buƙatar sa ido na musamman.
Kazalika ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta shirya domin yiwuwar kai hari “domin kawar da 'yan ta'adda masu kaifin kishin Musulinci waɗanda ke yin wannan ta’asa.”
Nan-take kalamansa suka soma tasiri a kasuwannin hannayen-jari. A kasuwar hannayen-jarin Nijeriya darajar kasuwar ta ragu da kashi 0.25 cikin 100 inda kasuwar ta ƙarƙare da maki 153,739.11 a ranar Litinin, lamarin da ya rage ribar shekara zuwa shekara zuwa kashi 49.37 cikin 100. Ƙimar kasuwar kuma ta ragu da naira biliyan 245.88, inda ƙimar ta tsaya a naira tiriliyan 97.58t.
Faɗuwar ta fi yawa ne daga yadda aka sayar da hanayen-jarin Aradel Holdings (kashi -9.21 cikin 100) da kuma Access Corporation (kashi -3.07 cikin 100). Ƙarfin gwiwar masu jari dai ya yi rauni inda farashin hannayen-jarinkamfanoni 38 inda farashin hannayen-jarin kamfanoni 19 suka faɗi.
Hannun-jarin kamfanin Union Dicon ne ya fi samun riba (kashi +9.93 cikin 100), yayin da farashin hannayen-jarin kamfanin Honeywell Flour Mills yake kan gaba a cikin waɗanda suka faɗi (kashi -10.00 cikin 100).
Kazalika hada-hadar hannayen-jari ta ragu sosai inda adadi da ƙimar hannayen-jarin da aka saya ko sayar suka faɗi da kashi 87.94 cikin 100 da kuma kashi 44.64 cikin 100, zuwa hannayen-jari miliyan 627.5 masu kimar naira biliyan N25bn. Bankin United Bank for Africa (UBA) ya fi mamaye harkar, inda aka yi musayar hannayen-jarinsa miliyan 136.8 (kashi 21.8 cikin 100 na adadin hannayen-jarin) wanda kimarsu ta kai naira biliyan N5.5bn (kashi 22.2 cikin 100 na adadin ƙimar kasuwar).









