Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙi
DUNIYA
3 minti karatu
Zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru yayin da ake yaƙiRahoton bincike da wata ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasar Switzerland mai suna Swissaid ta yi, ya nuna cewa kasar ta UAE ta shigar da kusan tan 29 na zinari daga Sudan, a shekarar 2024 idan aka kwatanta da tan 17 da ta shigar a shekarar 2023.
Wannan adadin fa bai haɗa da sauran adadin zinarin da ake zargin an kwasa daga Sudan an kai wasu kasashen kafin a shigar da shi Daular Larabawan.
5 awanni baya

Yayin da yakin basasar Sudan ke kazancewa, inda ake kashe mata da yara da tagayyara rayuwa dubban daruruwan al’ummar cikin Sudan, wani bincike ya bayyana cewa adadin zinarin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ke shigarwa ƙasarta daga Sudan ya ƙaru matuka.

Rahoton bincike da wata ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasar Switzerland mai suna Swissaid ta yi, ya nuna cewa kasar ta UAE ta shigar da kusan tan 29 na zinari daga Sudan, a shekarar 2024 idan aka kwatanta da tan 17 da ta shigar a shekarar 2023.

 Wannan adadin fa bai haɗa da sauran adadin zinarin da ake zargin an kwasa daga Sudan an kai wasu kasashen kafin a shigar da shi Daular Larabawan.

 Ƙungiyar agajin ta ruwaito wasu bayanan cinikayyar ƙasashen waje na UAE da aka wallafa a kundin bayanan Comtrade na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 31 ga Oktoban 2025. Sai dai Swissaid ta ce tuni aka cire waɗannan bayanan daga shafin da aka wallafa su.

 Haka nan, kasar da ke Gabas ta Tsakiya, ta shigar da tan 18 na zinari daga Chadi, sai kuma tan tara daga Libya, duka a bara.

UAE ita ce ƙasar da ta fi kowace kasa sayan zinari daga Afirka, inda ta shigar da tan 748 daga nahiyar a shekarar 2024 — karin kashi 18% idan aka kwatanta da abin da ta saya a 2023.

 Babu tabbaci kan takamaimiyar darajar zinarin da ƙasar ta shigar daga Afirka a lissafi kudi. Sai dai ƙungiyar Swissaid ta ce UAE ta sayi zinarin ƙasar Rasha da ya kai dala biliyan 5.4 a shekarar 2024.

 Haka nan kididdigar kasuwanci ta nuna cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa ita ce kasa ta biyu a duniya wajen shigo da zinari, inda take biye da Switzerland.

 Ƙaruwar safarar zinari daga Sudan zuwa Daular na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar da ke arewacin Afirka ke ci gaba da fama da yaƙin da ake tsakanin sojoji da kuma dakarun RSF.

 Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan aƙalla mutum miliyan 15 aka raba da muhallansu, tun bayan barkewar rikicin a watan Afrilu na shekarar 2023.

 Gwamnatin Sudan da ma Majalisar Ɗinkin Duniya sun zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da bayar da makamai ga dakarun RSF, amma kasar ta musanta wannan zargin.

 Yawancin zinarin Sudan yana fitowa ne daga yankunan arewa da yammaci, musamman yankin Darfur, da Kordofan ta Kudu, da Jihar Arewa — wato wasu daga cikin yankunan da yaƙin ya fi shafa.

 A shekarar 2023, ƙasar UAE da ke yankin Gulf ta samar da wata doka domin bin ƙa’idojin da Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci gaban Duniya ta shimfiɗa, wadda wata ƙungiya ce da ta ƙunshi ƙasashe masu arziki.

 A zahiri yake cewa, waɗannan ƙa’idojin sun haramta shigo da zinarin da aka samu ba ta halastacciyar hanya ba.