Ministan noma da dabbobi na Nijar, Kanar Mahaman Elhadj Ousmane , da takwaransa na ƙasar Chadi, ministan dabbobi da kiwo, Farfesa Abderahim Awat Atteib, sun kai ziyara Diffa ranar Litinin domin suka ƙaddamar da aikin haɗaka na rigakafi wa dabbobi kan cututtukan da ke addabar dabbobi.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar ta ruwaito cewa za a ƙaddamar da aikin ne ranar Talata a Diffa a wata unguwa da ake ce wa Sayam, a wani ƙauye mai suna Chétimari , a ƙarƙashin jagorancin ministocin biyu.
Yana da manufar ƙarfafa lafiya da kuma hadin kan makiyaya tsakanin Nijar da Chadi, ƙasashe biyu da ke da dangantaka ta ƙut da ƙut da na shekaru aru-aru musamman ta fannin dabbobi da makiyaya, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar.
Kazalika kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa shirin ya nuna niyyar ƙasashen biyu na haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar cututtukan dabbobi dake tsallake kan iyakokin ƙasashen biyu da kuma tsare hanyoyin samun makiyaya da masu kiwon dabbobi a ƙasashen biyu.
Wannan haɗin kai ta fagen lafiyar dabbobin dai wani ci-gaba ne na tattaunawar dangantaka da ƙasashen suka yi tsakanin ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2023, wanda ya mayar da hankali kan shirya gangamin rigakafin.
A ƙarshen wannan tattaunawar an cim ma yarjejeniyar shirya bikin ƙaddamar da gangamin rigakafin dabbobi da zai ratsa kan iyakan ƙasashen biyu a ko wace shekara a ɗaya daga cikin ƙasashen biyu wannan.
Ƙasar Chadi ce ta karɓi baƙuncin bikin ranar 27 ga watan Nuwamba na shekarar 2023 a Liwa a ƙarƙashin jagorancin ministocin ƙasashen biyu inda aka ƙaddamar da shirin rigakafi na haɗin gwiwa na farko domin rage yaduwar cututtukan dabbobi a kusa da kan iyakar ƙasar.
A zamansu a garin Diffa, ministocin biyu za su yi taron bita da ma’aikatan jinyan dabbobi da wakilan ƙungiyoyin masu kiwon dabbobi da kuma tattaunawa kan kaikomowar makiyaya ta kan iyakan ƙasashen biyu, domin zaman lafiya da wadatan makiyaya a yankin tafkin Chadi.







