Manchester City ta sanya hannu domin sayen ɗan wasan gaban Ghana, Antoine Semenyo, daga Bournemouth a ranar Jumma'a domin ƙara ƙarfafa ‘yan wasan gaba a ƙoƙarin ƙungiyar na neman kambin Premier League da Champions League.
Semenyo, wanda ya zura ƙwallaye 10 kuma ya kasance ɗaya daga cikin 'yan gaba mafiya ƙwarewa a ƙwallon kafa ta Ingila a wannan kakar, ya koma a kan yarjejeniya da ake cewa ta kai fam miliyan 65 (kimanin dalar Amurka miliyan 87) kuma yarjejeniyar ta yi tsawon shekaru biyar da rabi.
A halin yanzu zai shiga cikin jerin ‘yan gaban City waɗanda suka haɗa da Jeremy Doku, Omar Marmoush, Savinho da Oscar Bobb. Savinho da Bobb a halin yanzu suna jinya, yayin da Marmoush — wanda yake halartar Gasar Cin Kofin Afirka — bai samu farin jini a wannan kakar ba.
Semenyo mai shekaru 26 an kuma danganta shi da Manchester United da Liverpool. Ya shafe kaka biyu da rabi a Bournemouth bayan ya koma daga Bristol City.
“Ina da babbar dama ta ingantawa, ” kamar yadda Semenyo ya ce a cikin wata sanarwa ta City, don haka kasancewa a wannan kulob, a wannan matakin na aikina, ya dace sosai da ni. Girmamawa ce a kasance a nan.
“Mafi kyawun wasan ƙwallona zai zo nan gaba, na tabbata da hakan.










