KASUWANCI
2 minti karatu
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
An ɗauki wannan matakin ne domin a tabbatar da bin gaskiya da kuma halascin cinikayya na ƙetare.
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
Wannan matakin zai sa a iya bibiyar kuɗaɗen ƙetare da 'yan kasuwar ƙasar ke amfani da su.
29 Agusta 2025

Babban Bankin Ƙasar Ghana (BoG) ya fitar da sabon umarni wanda ke buƙatar masu shigar da kayayyaki da ke amfani da kuɗaɗen ƙetare su tabbatar cewa sun ba da bayanan da ake buƙata a rubuce, a wani ɓangare na matakan hana halatta kuɗin haram.

Umarnin, wanda Misis Aimee V. Quashie ta sanya wa hannu a madadin sakataren bankin, ya gyara ƙa’idojin shiga da fitar da kuɗaɗen ƙetare, kamar yadda kamfanin dillancin ƙasar Ghana ya rawaito.

Wani muhimmin ɓangare na gyaran ya mayar da hankali kan masu shigar da kayayyaki cikin ƙasar, waɗanda a yanzu ya zama dole su samar da wasu takardu domin amfani da kuɗaɗen ƙetare wajen ciniki a harkar kasuwancinsu.

Sanarwar ta BoG ta ce ana buƙatar masu shigar da kayayyaki ƙasar su gabatar da:” takardar shaidar ofishin kuɗin ƙetare da shaidar banki a matsayin hujjar cire kuɗin a banki ko kuma siyansa, da kuma takardar shiga da kaya da aka sanya wa hannu da rasiti da kuma kwantiragi.”

An ɗauki wannan matakin ne domin a tabbatar da bin gaskiya da kuma halascin cinikayya ta ƙetare.

Kazalika, matakin na nufin hana wanzuwar kuɗin haram ta hanyar samar da takardun da za a iya bibiya kan duk wata muhimmiyar cinikayya da masu shigar da kayayyakin ƙasar suka yi.

Sanarwar ta jaddada cewa ƙin bayyana kuɗaɗe da yin bayani na ƙarya ko kuma gaza gabatar da takardun da ake buƙata zai sa a ƙwace kuɗaɗen da ba a bayyana ba nan take, ko ƙaƙaba tara ko kuma gurfanarwa a gaban kotu.

Rumbun Labarai
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Kamfanin Orano na Faransa ya ce ya tara tan 1,500 na uranium a Nijar
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin Turkish Airlines zai sayi jiragen sama na Boeing 225 bayan Trump da Erdogan sun tattauna
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Matatar mai ta Dangote ta yi watsi da jita-jitar dakatar da aiki na wasu watanni
Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin kuɗin ƙetare na UBA da wasu manhajojin aika kuɗi
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoni
Kamfanin Tsaro na Turkiyya zai ƙulla yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaƙi
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Filin jiragen sama na Istanbul ya sake cirar tutar tashin jirage a Turai, in ji Ministan Sufuri
China da Amurka sun cim ma yarjejeniyar kasuwanci
Shugaban Nijeriya Tinubu ya sanya hannu a kan sababbin Dokokin Haraji