| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Trump ya saka ƙasashen Afirka biyar cikin jerin da ya haramta wa shiga Amurka
Matakin na ranar Talata ya haramta wa 'yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Sudan ta Kudu da Syria da kuma masu riƙe da takardar tafiya ta hukumar Falasɗinawa
Trump ya saka ƙasashen Afirka biyar cikin jerin da ya haramta wa shiga Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump yana ta rage damar shiga ƙasar ta hanyar bayar da umarni tun da ya koma kan ƙaragar mulki / Reuters
3 awanni baya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara wasu ƙasashe a kan jerin waɗanda aka haramta wa ‘ya’yansu shiga Amurka.

Fadar White House ta bayyana a ranar Talata cewa Trump ya sanya hannu kan wata sanarwa mai "faɗaɗa da kuma ƙarfafa tsaurara hana shiga wa ‘yan ƙasashen da suka nuna gazawa wajen tantancewa da kuma musayar bayanai domin kare ƙasar daga barazanar tsaro."

Matakin na ranar Talata ya haramta wa ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da Sudan Ta Kudu da Syria da kuma waɗanda suke riƙe da takardun tafiyar da hukumar Falasdinawa ta bayar.

Matakin ya kuma ƙaƙaba cikakken haramci kan ƙasashen Laos da Saliyo, waɗanda a da ƙwarya-ƙwaryar haramci aka ƙaƙaba musu.

Fadar White House ta ce haramcin da aka faɗaɗa zai fara iki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.

Shelar haramta shiga

Fadar White House ta yi ishara ga ƙin ficewa daga ƙasar bayan ƙarewar bizarsu a matsayin hujjar haramta wa ‘yan Syria shiga ƙasar.

"Syria na fitowa daga yaƙin basasar da aka daɗe ana yi. Yayin da ƙasar ke ƙoƙarin magance matsalolin tsaronta tare da Amurka, har yanzu Syria ba ta da hukuma ɗaya mai ƙarfi ta ba da fasfo ko kuma takardun fararen-hula kuma ba ta da makaman tantancewa da suka dace," in ji Fadar White House .

Trump ya rattaba hannu kan wata sanarwa a watan Yuni da ta haramta wa ‘yan ƙasashe 12 shiga Amurka da kuma taƙaita wa ‘yan ƙasashe bakwai damar shiga Amurka, yana mai cewa ana buƙatar hakan domin kariya daga "‘yan ta’addan ƙetare" da kuma wasu barazana na tsaro.

Haramta shigar za ta yi aiki ne kan masu zuwa zama a ƙasar da ma wadanda ba su da niyyar zaman a ƙasar kamar masu yawon buɗa ido da ɗalibai da ‘yankasuwa matafiya.

Har yanzu haramcin tafiyar na nan a ƙasashe sha biyun, in ji Fadar White House .

Trump ya kuma ƙara ƙwarya-ƙwaryar taƙaitawa da kuma taƙaita shiga kan ƙarin ƙasashe 15, ciki har da Nijeriya, wadda Trump ke bincike a kanta bayan ya yi barazanar kai mata hari a farkon watan Nuwamba game da zargin muzguna wa Kiristoci a ƙasar.

Nijeriya ta ce iƙirarin da ake yi cewa Kiristoci na fuskantar zalunci da danniya na murɗa wani yanayi na tsaro mai sarƙaƙiya ne kuma ya ƙi bayyana ƙoƙarin da ake yi na kiyaye ‘yancin addini.

Tun lokacin da ya koma karagar mulki a watan Janairu, Trump ya mayar da hankali sosai wajen ɗaɓɓaka dokokin shige da fice, inda ya tura jami’an gwamnatin tarayya zuwa mahimman biranen Amurka tare da hana masu neman mafaka shiga ƙasar daga kan iyakar Amurka da Mexico.