Dubban ɗaruruwan mutane ne suka yi gangami a birnin Istanbul domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, inda suka yi kira a kawo ƙarshen yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza.
Gangamin wanda shugabannin addini da na ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam suka jagoranta mai taken "Ba Za Mu Yi Shiru ba", wato “We Do Not Remain Silent” a Turancin Ingilishi ya samu halartar ƙungiyoyi fiye da 400.
Mahalarta gangamin sun fito da asalatu ranar Alhamis inda suka soma da gudanar da sallar asubahi a manyan masallatan da suka haɗa da Ayasofya Grand Mosque, Sultanahmet, Fatih, Suleymaniye, da Eminonu Yeni Cami.
Daga nan, masu gangamin sun yi maci zuwa Gadar Galata, riƙe da tutocin Turkiyya da na Falasɗinu, kuma sanye da ƙyallayen Falasɗinawa waɗanda aka rubuta kamar “Daga Istanbul zuwa Gaza, dubban gaisuwa ga masu gwagwarmaya” da “A ‘Yanta Falasɗinu.”
Bilal Erdogan, shugaban Gidauniyar İlim Yayma, ya gabatar da jawabi ga mahalarta gangamin, inda ya jaddada goyon bayansu ga Falasɗinawa.
“Duk shekara, masu halartar irin gangami suna ƙara yawa, kuma a yau muna jin ƙarfi na ‘yan’uwantaka a matsayinmu na ‘yan ƙasa,” in ji shi, inda ya yi addu’o’i na samun ‘yanci ga mutanen da ke Falasɗinu da Birnin Ƙudus.
Sauran shugabannin ƙungiyoyin fararen-hula, waɗanda suka haɗa da Abdullah Ozdemir, shugaban AK Party reshen Istanbul, da shugaban ƙungiyar ONDER İmam Hatipliler Abdullah Ceylan, sun halarci macin.
Mahalarta gangamin sun riƙe kwalaye da aka rubuta “A Yi Adalci ga Falasɗinu” inda suka riƙa rera take na yin Allah wadai da Isra’ila.
Mutane sun riƙa raba shayi da biredin simit da miya a kan hanya ga masu gangamin.
‘Yansanda sun ƙarfafa matakan tsaro a kan hanya, ko da yake waɗanda suka shirya gangamin sun bayyana shi a matsayin wanda aka yi cikin lumana domin goyon bayan Falasɗinawa.
Mahalarta da dama sun bayyana fatan ganin shekarar 2026 ta kasance mai cike da adalci da zaman lafiya ga al’ummar Gaza da ke cikin uƙuba, inda suka bayyana gangamin a matsayin “babban saƙo na goyn baya” daga Istanbul ga duniya.

























