TURKIYYA
2 minti karatu
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Mambobin ƙungiyar ta'addanci ta PKK sun yi wannan sanarwar ne a Sulaymaniyah da ke Iraƙi, wanda hakan wata alama ce ta babban ci gaba a shirin “Turkiyya Mara Ta’addanci”
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
An yi bikin ƙona makaman mayaƙan PKK a Sulaymaniyah da ke Iraƙi a ranar 11 ga Yulin 2025. / Reuters
26 Oktoba 2025

An samu wani babban ci gaba a ranar Lahadi a cikin shirin “Turkiyya Mara Ta’addanci” na Ankara, yayin da ƙungiyar ta’addanci ta PKK ta sanar da cewa tana janye dukkan dakarunta daga Turkiyya zuwa arewacin Iraki.

Kungiyar ta’addanci ta PKK ta bayyana a cikin wata sanarwa da aka karanta a yankin Qandil na Sulaymaniyah a arewacin Iraki cewa tana aiwatar da janye dukkan dakarunta daga cikin Turkiyya.

Sanarwar ta bayyana cewa an yanke shawarar kawo karshen kasancewar kungiyar a matsayin mai dauke da makamai da ayyukanta a watan Mayu, bisa umarnin jagoranta da ke tsare, Abdullah Ocalan.

Wata tawaga ta mutum 23 daga cikin ‘yan ta’addan PKK da aka ce sun iso daga Turkiyya sun halarci wurin da aka yi wannan sanarwa.

A watan Yuli, wata tawaga daga cikin mambobin PKK sun lalata wani rukuni na farko na makamai, wanda Turkiyya ta bayyana a matsayin “muhimmin mataki da ba za a iya komawa baya ba.”

Kungiyar, wadda Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci, ta shafe shekaru da dama tana gudanar da ayyukan ta’addanci a Turkiyya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tun daga shekarun 1980s.

Efkan Ala, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Adalci da Ci Gaba (AK Party), ya ce sanarwar da matakan da aka dauka kwanan nan suna nuna “wani babban mataki da aka wuce wajen kawar da ta’addanci.”

“Da zarar an kawar da ta’addanci gaba daya, wanda ya dade da zama tarnaƙi a kafufuwanmu, za a bude kofar wani sabon zamani,” in ji shi.

Mai magana da yawun AK Party, Omer Celik, ya ce ci gaba da rushewa da kuma dakatar da tsarukan daukar makamai na PKK a Turkiyya, Iraki da Syria suna nuna sakamako na ainihi na shirin “Turkiyya Mara Ta’addanci.”

Ya bayyana shirin a matsayin “mataki na dabaru da tarihi don kare dimokuradiyyarmu daga duk wata barazana,” yana mai cewa wannan alama ce ta “tsayin daka kan yunkurin da ake yi na kakaba wa yankin tasirin ƙungiyoyin ta’addanci.”

Celik ya ce wannan tsari, wanda Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta da karfin shugabanci na kasa, tare da jagorancin Kwamitin Hadin Kai, ‘Yan Uwa da Dimokuradiyya na Majalisar, “yana ci gaba da samar da sakamako masu kyau.”

Ya kara da cewa Turkiyya tana ci gaba da kasancewa cikin shiri don dakile duk wani yunkuri na tayar da hankula a yankin, ciki har da kokarin siyasa, leken asiri da na aiki don lalata wannan tsari.