| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Turkiyya ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashe waje a kan Iran – Erdogan
Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce kwanciyar hankalin yankin da kuma tausasan kalamai su ne suka fi muhimmanci a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a faɗin ƙas Iran.
Turkiyya ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashe waje a kan Iran – Erdogan
Shugaba Erdogan ya jaddada cewa Ankara tana adawa da duk wani tsoma baki na ƙasashen waje a harkokin Tehran. / TRT World
21 awanni baya

Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan ya shaida wa takwaransa Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ta waya cewa ba ya goyon bayan tsoma baki da wasu ƙasashe suke yi kan zanga-zangar da ake yi a Iran, kuma ya ce yana martaba zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ƙasashe makwabtan Turkiyya suke ciki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Turkiyya ta bayyana a shafinta na X.

A wata sanarwa ta ce Shugaba Erdogan ya tattauna da shugaban kan abubuwan da suke faruwa a Iran a baya bayan nan. Sannan Shugaba Erdogan ya ce Turkiyya tana so a warware matsalolin da ke faruwa ba tare da sun ƙara taɓarɓarewa ba.

Iran tana fama da zanga-zanga adawa da gwamnati irin wacce aka daɗe ba a fuskanci irinta ba a tarihin ƙasar.

Kuma sakamakon murƙushe masu zanga-zangar da ake yi ya jawo “mutuwar mutum dubu bakwai” kamar yadda Jagoran Addinin Ƙasar Ali Khamenei ya bayyana a ranar Asabar.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran ta sha alwashin gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta yi gangancin kai wa Khamenei hari

Wannan ne karon farko da jagoran addini na Iran ya yi magana kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu wanda ya ɗora alhakin hakan a kan ƙasar Amurka.

Zanga-zanga da yajin aiki sun jawo tattalin arzikin ƙasar ya faɗa matsanancin hali wanda sakamakon haka ya sa aka fara zanga-zanga adawa da malaman addini da ke shugabantar ƙasar tun bayan juyin juya halin shekarar 1979, inda mutane suke ci gaba da yin zanga-zanga a kan tituna wacce aka fara tun daga ranar 8 ga watan Janairu.

A ranar Laraba ministan harkokin wajen Iran ya aika da saƙon gargaɗi kai-tsaye ga Amurka, inda ya ce Jamhuriyar Musuluncin “za ta mayar da martani da duk wani abu da muke da shi idan aka kai mana sabon hari.”

Alƙaluman farko da hukumomin kasar suka fita a wata sanarwa da gidauniyar ’yan mazan jiya da shahidai suka fitar ta ce zuwa ranar Laraba mutum 3,117 ne aka kashe yayin zanga-zangar.