| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Gwamnatin Burkina Faso ta rusa dukkan jam’iyyun siyasar kasar a ƙoƙarin ƙara ƙarfin iko
Shugabannin mulkin sojin Burkina Faso sun ce ana buƙatar rusa jam’iyyun ne don samar da haɗin kai da kawo sauye-sauye a yayin da ake ta jinkirta gudanar da zaɓe har sai baba ta gani.
Gwamnatin Burkina Faso ta rusa dukkan jam’iyyun siyasar kasar a ƙoƙarin ƙara ƙarfin iko
Burkina Faso ta kasance a karkashin mulkin soji tun Satumban 2022 bayan da Kyaftin Traore ya kwace mulki / Reuters
4 awanni baya

Gwamnatin Burkina Faso da sojoji ke jagoranta a ranar Alhamis ta ba da umarnin rusa dukkan jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyi, lamarin da ke nuna ƙaruwar ƙarfin iko na gwamnatin soja kusan shekaru uku bayan ƙwace mulki.

Wannan doka, wadda aka amince da ita a lokacin taron majalisar ministoci na mako-mako wanda shugaban sojoji Ibrahim Traore ya jagoranta, ta kuma ba da umarnin a mayar da kadarorin jam'iyyun da aka rusa zuwa ga gwamnati.

Hukumomi sun ce an shirya daftarin dokar don soke dokokin da ke da su waɗanda ke kula da harkokin kuɗi da ayyukan jam'iyyun.

Masu AlakaTRT Afrika - Burkina Faso: Dalilan da suka hana a samu zaman lafiya

Ministan Kula da Yankuna Emile Zerbo ya ce matakin ya biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin "cikakkiyar fahimtar" nuna ɓangarancin jam’iyyun siyasar ƙasar.

"Wannan babban mataki mai muhimmanci wani ɓangare ne na sake gina ƙasar," in ji Zerbo, yana mai jaddada cewa jam'iyyun siyasa sun kauce daga hurumin da doka ta ba su kuma suna bayar da gudunmawa wajen raba kan jama’ar ƙasa.

‘Kare Haɗin Kan Ƙasa’

Gwamnati ta ce yawaitar jam'iyyu ya haifar da rarrabuwar kawuna, ya raunana haɗin kan al'umma, ya kuma lalata ingantaccen shugabanci.

Rusa su, a cewarta, an yi shi ne don "kiyaye haɗin kan ƙasa, ƙarfafa haɗin kan ayyukan gwamnati, da kuma share fagen yin garambawul ga tsarin mulkin siyasa."

Burkina Faso ta kasance ƙarƙashin mulkin soja tun lokacin da Traore ya jagoranci juyin mulki a watan Satumbar 2022, juyin mulki na biyu a wannan shekarar. Gwamnati ta sha ambatar yanayin tsaro da ke taɓarɓarewa a ƙasar - wanda 'yan ta’adda masu alaƙa da al-Qaeda da Daesh suka jagoranta - don ba da hujjar ɗaukar matakai na musamman.

An ɗage zaɓen da aka yi alƙawarin yi a watan Yulin 2024 har abada, kuma an dakatar da ayyukan jam'iyyun siyasa bayan juyin mulkin, ko da yake ba a haramta su ba a hukumance har zuwa yanzu.