Hukumomin Portugal sun gurfanar da matar tsohon shugaban Guinea-Bissau da aka hamɓarar a matsayin wani ɓangare na bincike kan zargin shigo da kuɗi ba bisa ka'ida ba da karkatar da kuɗi, in ji 'yansanda ɓangaren shari'a a ranar Talata.
Dinisia Reis Embalo, matar Umaro Sissoco Embalo, ta isa Lisbon a cikin jirgi daga Guinea-Bissau tare da wani fasinja wanda jami'an Portugal suka kama a ranar Lahadi bayan wani bayanin asiri.
An ce wannan fasinjan, wanda yake ɗauke da tsabar kuɗi kusan euro miliyan biyar ($5.9m), ana zargin sa da shigo da fasa-ƙwautin kuɗi, in ji 'yansanda a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun 'yansandan ɓangaren shari'ar ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tuhumar Dinisia Reis Embalo tana da "alaƙa" da wannan binciken, ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.
An ayyana shi a matsayin 'jirgin soja'
Da farko an bayyana jirgin da ya ɗauki mutanen a matsayin na soja, kuma an shirya cewa zai zarce zuwa garin Beja a kudancin Portugal.
Sai dai, "daga bisani an tabbatar da cewa yanayin jirgin da makomarsa sun bambanta", in ji 'yansandan a ranar Talata.
Kafofin watsa labaran Portugal sun ruwaito cewa wanda aka fara zargi mutum ne mai kusanci da shugaban Guinea-Bissau da aka kifar, Embalo, wanda ya gudu bayan sojoji sun kifar da shi a juyin mulkin 26 ga Nuwamba.
Gidan talabajin na gwamnati RTP ya bayyana shi a matsayin ɗan kasuwa Tito Gomes Fernandes.
Ministan Harkokin Wajen Portugal Paulo Rangel ya faɗa a ranar Talata cewa yana tuntuɓar hukumomin Guinea-Bissau wajen ƙoƙarin samo hanyar "komawa ga tsarin mulki."














