| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Burkina Faso, Nijar da Mali sun buɗe bankin zuba jari domin samar da ababen more rayuwa
Ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), wato Burkina Faso, Nijar da Mali sun buɗe bankin zuba jari da ci-gaba ranar Laraba domin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da ci-gaban tattalin arzikin yankin.
Burkina Faso, Nijar da Mali sun buɗe bankin zuba jari domin samar da ababen more rayuwa
Ƙasashen uku sun sanar da cewa sun saka $895m a cikin bankin a matakin farko / Other
19 Disamba 2025

Ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), wato Burkina Faso, Nijar da Mali sun buɗe bankin zuba jari da ci-gaba ranar Laraba domin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da ci-gaban tattalin arzikin yankin.

Ministan Tattalin Arziki da Tsare-Tsare na Burkina Faso Aboubakar Nacanabo ya sanar da cewa sun saka $895m a cikin bankin a matakin farko, bayan ganawar da ya yi da takwarorinsa na ƙasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.

Masu AlakaTRT Afrika - Sahel Alliance: Nijar, Burkina Faso da Mali sun kulla kawance

A watan Mayun da ya gaba ne, ƙasashen uku suka sanar da wani gagarumin shiri na kafa bankin zuba jari da zai riƙa daukar nauyin gudanar da manyan ayyukan more rayuwa da ci-gaba na ƙasashen uku.

Kasashen sun kafa ƙungiyar ƙawance ta Alliance of Sahel States a yayin da dukkansu suke rigima da ECOWAS sakamakon juyin mulkin da aka yi a Nijar.

"Wannan kawancen zai kasance na soji da tattalin arziki tsakanin ƙasashen uku", a cewar Ministan Tsaron Mali Abdoulaye Diop a yayin taron manema labarai a wancan lokaci.