Kun taɓa sanin cewa akwai wani yanki a wannan duniyar tamu ta Earth da rana ba ta fitowa har tsawon kwanaki 60.
Wannan ba labarin almara ba ne irin wanda ake tsorata mu da shi da muna yara a ce “a yafi juna za a yi dare biyu”, wannan gaskiyar abin da ke faruwa ne ga mazauna yankunan arewacin Alaska da ke Amurka a duk lokacin hunturu. Ana kiran wannan al'amari da “Polar Night”.
“Polar night” ko Daren Polar wani yanayi ne da ke faruwa sakamakon karkatar da duniyarmu ke yi a sandar da take yin mazari a jiki, wato axis. Daren na faruwa ne a yankunan da ke ƙololuwar arewacin duniya, wato samanta a yadda muke a taswirarta, shi ne yankin da ake kira Turken Arewa, ko “North Pole”.
Sai kuma a duk wani wuri da ke arewacin Layin Arctic, nan ma Rana takan ɓace gabaɗaya, yadda ba a hango ta daga maƙurar gani, wato horizon tsawon lokaci a lokacin hunturu.
A Alaska, wannan yana faruwa ne a wurare kamar Utqiagvik, wani birni mafi nisa a arewacin ƙasar. A wajen, wannan lamarin kan faru ne duk shekara, inda a bana mazauna yankin suka ga faɗuwar rana ta ƙarshe a shekarar 2025, ranar 18 ga Nuwamba.
Ba za su sake ganin rana ba har sai ranar 22 ga Janairun 2026. Ma’ana za su shafe kusan kwanaki 65 a cikin duhu ba hasken rana.
Amma wannan yanayi na Polar Night ba wai yana nufin duhu dunɗim za a gani ba a koyaushe! Ranar ba ta yin nisa sosai daga maƙurar gani a sararin samaniya. Ke nan akwai wasu sa'o'i a kowace rana da ake ɗan ganin haske-haske da ake kira Jijjifin Salama ko “Civil twilight”.
Wannan haske ne marar ƙarfi, shuɗi shar, wanda zai isa a iya gani ba tare da kunna fitila ba.
Cakuduwar hasken ba ta da yawa, ma'ana mazauna yankin suna ganin wasu abubuwa masu ban mamaki a sararin samaniya, ciki har da hasken nan mai kyawu da ake kira “Northern Lights” ko “Aurora Borealis”, wato hasken da ke samuwa sakamakon kaɗawar iska a cikin tartsatsin sanyi.
Ta yaya mutanen wannan yanki ke rayuwa da jure wa yanayin?
Rayuwa ba ta tsayawa. Makarantu, harkokin kasuwanci, da dukkan muhimman ayyuka suna ci gaba kamar yadda aka saba. Al'umma suna mai da hankali kan ayyukan cikin gida da kuma shirin tarbar lokacin da hasken Rana zai dawo.
A takaice dai wasu al’ummar yankin da dama kan ce bacci ya ma fi daɗi a irin wannan lokacin, inda suke yin sa har da saleɓa, musamman tun da ga ɗumin na’urar ɗumama ɗaki da ke taimakawa wajen rage musu jin tsananin sanyin yanayin.
Babban ƙalubalensu shi ne tasirin da hakan ke yi kan zamantakewa da halayya da tunanin mutane.
Rashin hasken rana na iya haifar da matsaloli da ke hana kazar-kazar a wasu lokuta wato (Seasonal Affective Disorder ko SAD), har ma da sanya wasu a yanayi na tsananin damuwa.
Mazauna yankin sau da yawa suna amfani da fitilun haske na musamman da kuma cin abubuwa masu ɗauke da sinadaran Vitamin D don yaƙar wannan tasirin, suna kuma daidaita jadawalinsu da harkokin da suka shafi al'umma, ba tare da biye wa rashin ganin hasken rana ba.
A lokacin da wannan yanayi zai zo ƙarshe, rana za ta fito a ran 22 ga Janairun 2026. Hakan bai taƙaita ga fitowar rana ba kawai, ga al’ummar wannan yanki, ranar takan zama ta gagarumin shagalin murnar dawowa cikin hayyaci!
Ranar takan nuna ƙarshen dogon dare, amma fa daga lokacin za su fara lissafin wasu kwanakin da za a shiga na dogon yini, inda Rana ba ta faɗuwa sam har a lokacin da ya kamata a ce Tsakar Dare ne, abin da ake kira “Midnight Sun” a lokacin bazara.
Daren Polar Night, hujja ne da ke nuna ainihin al’ajabin kimiyyar duniyarmu da kuma juriyar da mutane mazauna yankin Arctic na Alaska ke da ita.
















