Gwamnatin Jihar Kano da ke Nijeriya ta dakatar da wasu likitoci da ake zargi da yin sakaci da aikinsu lamarin da ya yi sanadin mutuwar wata mata mai juna biyu.
Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar ta amince da cewa mutuwar Aishatu Umar, mai ‘ya’ya biyar, na da alaƙa da sakacin likitoci a asibitin Kula da Masu Yoyon Fitsari na Abubakar Imam da ke Kano.
A cikin wata sanarwa, Jami'ar Hulɗa da Jama'a ta Hukumar Samira Suleiman, ta ce binciken farko da Sakataren Zartarwa, Dakta Mansur Mudi Nagoda ya umarta, ya tabbatar da cewa an bar almakashi na tiyata a cikin jikin majiyyaciyar bayan an yi mata tiyata.
Hukumar ta sanar da dakatar da ma'aikata uku da ke da hannu kai-tsaye a lamarin daga ayyukan asibiti nan-take.
Ta kuma miƙa lamarin ga Kwamitin Ɗa'a na Lafiya na Jihar Kano don ƙarin bincike da ɗaukar matakan ladabtarwa bisa ga ƙa'idoji da dokokin aikin likitanci.

"Hukumar tana miƙa ta'aziyyarta ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kuma yi musu alhini kan wannan rashi mai raɗaɗi. Muna tabbatar wa jama'a cewa ba za a lamunci sakaci ta kowace hanya ba," in ji sanarwar.
Rahotannin da aka tattara sun bayyana cewa Aishatu Umar ta mutu bayan da aka yi zargin likitoci sun bar almakashi a cikinta bayan an yi mata tiyata a Cibiyar Kula Masu Yoyon Fitsari ta Gwamnati da ke Kano.
Mijinta, Abubakar Muhammad, ya ce matarsa ta fuskanci matsaloli masu tsanani bayan tiyatar, wanda daga ƙarshe ya kai ga mutuwar ta duk da ƙorafin da aka yi ta yi a asibiti.
Lamarin ya haifar da fushi tsakanin mazauna jihar kuma ya sanya damuwa game da rashin kulawa da kuma ɗaukar nauyin da ya dace a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati.
Mutane da yawa daga cikin 'yan Najeriya sun kuma yi ta kira da a yi adalci ga mamaciyar da kuma gyara tsarin kiwon lafiya.








