20 Oktoba 2025
Kocin Real Madrid, Xabi Alonso ya yaba wa zaƙaƙurin ɗan wasan gaba ƙungiyar Vinicius Jr, saboda rawar da ya taka a wasan da suka doke Getafe da ci 1-0.
Wasan bai yi wa Getafe daɗi ba saboda ta ƙare ne da ‘yan wasa 9 a fili, sakamkon sallamar ‘yan wasanta biyu da aka yi.
Duk da wannan fifiko, Real Madrid ba ta ji da daɗi ba saboda da ƙyar ta samu nasarar zuwa ƙwallo a mintunan ƙarshe na wasan ta hannun Kylian Mbappe.
Za ku so karanta wadannan
A minti na 77, Vinicius Jr ya tunzura ‘yan wasa Getafe har ya janyo aka ba wa Allan Nyom, ɗan wasan bayan Getafe jan kati, minti ɗaya da shigowarsa fili.
Minti 7 bayan nan, Vinicius ya sake shiga wata sa’in’sa da wani ɗan wasan Getafe, Alex Sancris, wanda ya janyo mas samun yalon kati karo na biyu, wanda ya janyo sallamar sa.