Hukumar ta ce ta ɗauki matakin bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar fim. / Hoto: Abba El-Mustapha

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta shirya fina-finai da ke nuna fadan daba da harkar Daudu a Kano.

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da hukumar ta tace fina-finan ta fitar a ranar Laraba.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta tattauna da ma’aikatan hukumar da wasu daga cikin wakilan yan masana'antar shirya fina-finan ta kannywood waɗanda suka haɗa da kungiyoyin MOPPAN, Arewa Film Makers da daraktoci da kuma furodusoshi.

Abba ya kara da cewa doka ce ta bai wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin ya ci karo da tarbiya tare da al'adar al'ummar da ke jihar.

“Tuni lokaci ya shige da za'a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaɗuwa a cikin al'umma,” in ji shi.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta ɗauki matakin rufe gidajen gala a jihar inda ta ce har sai bayan azumin watan Ramadana.

TRT Afrika