| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
APC ta yarda Akpabio ya zama shugaban Majalisar Dattawa, Barau ya zama mataimakinsa
APC ta mika kujerar shugaban majalisar dattawa ga Kudu Maso Kudu yayin da ta ware kujerar mataimakinsa ga Arewa Maso Yammacin Nijeriya.
APC ta yarda Akpabio ya zama shugaban Majalisar Dattawa, Barau ya zama mataimakinsa
Jam'iyyar ta fitar da Sanata Akpabio da Sanata Barau a matsayin shugaban majalisar dattijai da mataimaki /Hoto: Akpabio/Barau Facebook / Others
8 Mayu 2023

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana yadda tsarin shugabancin Majalisar Dokokin kasar karo na 10 zai kasance.

A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a ranar Litinin a Twitter, ta ce Kwamitin Zartarwar ta ya cimma matsayar ce bayan ya gana da zababben shugaban Nijeriya mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki na APC.

Sanarwar ta ce ta “girmama sakamako da matsayar da aka cimma a taron da ya gudana tsakanin zababben shugaban kasa da shugabannin Kwamitin Zartarwar APC.”

Sannan ta yi kira da a cigaba da tuntuba da masu ruwa da tsakin da suka kamata don tabbatar da cewa an samu goyon bayan masu neman takarar shugabancin Majalisar Dokokin a fadin kasar da cikin jam'iyyar.

An mika shugabancin Shugaban Majalisar Dattijai ga yankin Kudu maso Kudu – Sanata Godwill Akpabio daga Jihar Akwa Ibom.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai daga Arewa maso Yamma – Sanata Barau Jibrin daga Jihar Kano.

Shugaban Majalisar Wakilai daga Arewa maso Yamma - Honorabul Abbas Tajuddeen daga Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai daga Kudu maso Gabas – Honorabul Ben Kalu daga Jihar Abia.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda