( Tun daga shekarar 2021 ne ɗan wasan barkwanci na kasar Uganda Funny Nad ya soma fice a kafar Tiktok a shekarar 2021. Hoto: Darakta Edrine    

Daga Pauline Odhiambo

Dariya har cikin zuciya tare da barkwanci da kuma nishadi tamkar magani ne ga ruhi, kana ga mai barkwanci a kafar TikTok Mutaka Abdulrahim Burshir wanda aka fi saninsa da ‘Funny Nad’ zuwa ga mabiyansa, dariya ita ce warakar da ke magance matsalar damuwa.

Sai dai Mutaka bai yi wani shiri zuwa ga shahararsa ba. Ya kasance yana aiki a shagon intanet na kawunsa, inda a lokacin ɓullar annobar Covid-19 dabarar ƙirƙirar mutum mai ban dariya ta zo masa.

Zaman kulle na cutar Covid-19 ya katse masa karatunsa da yake yi na aikin jinya, sakamakon bakin cikin rasa kawunsa da kakansa sanadin ciwon sukari yasa bayan wasu ‘yan watanni Mutaka ya nemi bin hanyar barkwanci domin saukakawa ruhinsa.

Mutaka ya shirya bidiyo da dama a lokacin zaman kullen, yawancinsu na rawa a wakokin da suke tashe a kafafen sada zumunta.

Yaki da damuwa

"Na shahara ne bayan na wallafa bidiyoyi sama da 300a shafin Tiktok amma ba wai na yi niyya ko Shirin shahara ba ne. kawai dai ina hada bidiyon ne ga kaina don rage yawan damuwa da tunani da na ke fama da su,’’ kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka.

Sanya sutura ta yin barkwanci don sauya kamanninsa zuwa Funny Nad abu ne da ya zo masa cikin sauki.

Wata Riga da wando mai launin ruwan kasa na kawunsa da ya mutu ya bari da kuma wani baƙin maɗauri na wuya da ake makalawa a saman riga wadda wani abokinsa ya bashi kyauta suna daga cikin kayan da ya fara sanyawa. Shigar ta canza masa kamani sosai inda ya hada da wata ƙatuwar riga kwat wacce ta dan yi masa yawa da kuma takalmi mai launin Ruwan kasa na mahaifinsa.

Tufafin da Funny Nad ya samo asali ne daga kayan da mahaifinsa da kawunsa suka bas hi kyauta. Hoto: Director Edrine

Kofin barkwanci

Abinda kawai ya 'zabi kansa' shine kofin roba wanda yanzu ya zama wata muhimmiyar siffa ta Funny Nad.

"Ina daukar bidiyon wani barkwanci ne sai kwatsam na ji ƙishirwa, sai na nemi ƙanwata ta ba ni ruwa, sai ta zo da shi a cikin wani ɗan ƙaramin kofi," Mutaka ya tuna, ya ƙara da cewa sunansa na barkwanci ya samo asali ne sakamakon daga irin rawar da ya yi a makarantar sakandare.

"Kafin na ankara, na nadi gaba daya bidiyon barkwancin nawa rike da kofi a hannu, kuma ban lura da hakan ba sai lokacin da aka zo tacewa, kuma a lokacin an riga an makara a ce za a yi wani abu game da shi."

Ya dora bidiyon, kuma ya bazu cikin 'yan sa'o'i kadan bayan haka, an kalle shi fiye da sau miliyan uku zuwa yanzu.

"Mabiyana sun dauki kofin n aroba a matsayin wani abin kayatarwa, don haka na ci gaba da amfani da shi a duk bidiyon da nake yi. Yanzu ya zama wani ɓangare na tambari na," in ji shi.

Daga baya ya kara hula hana sallah mai launin shudi da fari, da buhun zuwa siyayya a cikin kayan da ya ke amfani da su a bidiyonsa.

Bidioyin Funny Nad wanda ya yasu sosao a TikTok an kalle shi fiye da sau miliyan 3. Hoto: Director Edrine

Funny Ned ya wallafa fiye da bidiyo 2,000 a TikTok sannan ya ma wallafa wasu a sauran kafofin sa da zumunta har da YouTube. Mafi yawan bidiyoyinsa na barkwanci ne inda yake mayar da hankali kan soyayya – wani batu da yace ya dace da abin da wadanda suke bibiyarsa suke so.

“Idan na yi bidiyon barkwanci dangane da yanda aka shammaci masoyi, ko da ba a shammace ka ba yau, na san cewa za a shammace ka gobe, to wannan bidiyo na barkwanci zai dace da kai a wannan lokaci” a cewarsa. Wannan shi ne abu mai kyau dangane da yin abin da ba a daina yayinsa.”

A hankali ya fadada irin bidiyoyin da yake yim da suka hada barkwanci dangane da hada karatu da aiki, yana mai karkatar da barkwancin nasa ta yadda zai samu karbuwa a wajen mutane masu shekaru daban-daban.

Mutaka ya ce a farko wasu daga yan gidansu sun damu da cewa barkwancinsa zai yi tasiri akan fatansa na zama malamin jinya, damuwar da suka nuna wa iyayensa a lokacin da bidiyon da yake samarwa suke kara samun karbuwa.

“Wasu daga cikin dangina sun yi zaton barkwancin da nake yi zai hana ni kammala karatuna na aikin jinya, sai suka yi wa iyayena magana dangane da haka. Amma da na nunawa iyayen irin bidiyon da nake yi, sai suka ga abin dariya ne kuma suka karfafa min gwiwa,” a cewarsa.

Daya daga ‘yan uwan mahaifinsa ya ma fi kowa ba shi goyon baya, ya amince cewa wata ran Mutaka zai zama wani fitacce.

Funny Nad ya samu kyautuka da dama saboda barkwancinsa. / Photo: Director Edrine

Neman taimakon kamfanonin duniya

Mutaka, wanda ya kammala karatunsa da takardar shaidar aikin jinya a shekarar 2024, ya shiga cikin mutane masu tasiri na Uganda da suke amfani da basirarsu don isar da sako ga masu masu bibiyarsu ta hanyar tallata kayayyaki daban-daban.

Ya yi aiki tare da wasu kamfanoni da suka hada da wani kamfanin lemo na kasa da kasa wanda ya nemi ya taimaka masa wajen fadada kasuwancinsa a Uganda.

"Mutane sukan yi min kuskuren daukata a matsayin dan Afirka ta Kudu ko dan Najeriya ko dan Kenya, kuma ina ganin hakan ya faru ne saboda ina yin abubuwana da harshen Ingilishi da ake magana da shi a kasashen Afirka da dama," in ji shi.

“Kusan kashi 40% na mabiyana ‘yan Afirka ta Kudu ne. 'Yan Uganda su ne kusan kashi 24% na masu kallo na, yayin da sauran masu kallo na ke kasashe daban-daban."

Hada burinsa na aikin jiya da kuma barkwanci shi ma ya kasance abu ne ‘mai kayatarwa’ ga Mutaka.

“Ina jin daɗin aikin jinya sosai domin ina son ba da magani, ina ba su dariya da kuma ganin yadda suke samun sauki,” in ji ma’aikaciyar jinya da ta ba da kai a wani asibitin gwamnati a Uganda.

"Hada aikin jinya da wasan kwaikwayo yana sa ni farin ciki, saboda kirkirar bidiyo wani abu ne da nake jin daɗinsa shi ma."

Abin da yake karfafa wa Mutaka gwiwa shi ne sanin cewa zai iya sa mutane farin ciki da dariya a duka ayyukan nasa biyu.

Zama fitacce ya taimaki Funny Ned ya samu mabiya mabambanta Hhoto: Director Edrine

Lashe kyautuka

“Na fara samar da bidiyo don in ringa sa kaina farin ciki a lokacin da abubuwa suka yi min yawa, sai na bige da da sa mutane dariya,” a cewarsa.

Mutasa da dama a Afirka suna fama da matsalolin damuwa, don haka ya yi magana a karkashin bidiyon da na sa yace na faranta masa rai a wanna rana, wannan yana kara min wani irin karfi na in kara yin wani bidiyon.”

Masu mugun nufi a harkar intanet sun so su dankwafe shi, amma Mutaka ya ci gaba da bunkasa duk da irin kalamai marasa dadi da suke yi masa.

“Irin wadannan mugun nufin ya yi kamari a duk lokacin da bidiyona ya yadu kamar wutar daji. Wasu kalaman da ake yi a kasan bidiyon ba su da dadin ji har na kan ji kamar in daina kawai,” kamar yadda ya fada wa TRT Afirka. “Na yanke shawarar kawai in manta da kalaman nasu marasa dadi, saboda idan na mayar da hankalina kansu, to wannan abin zai ci gaba da girmama, ya kuma kawo tsaiko wajen ci bunkasata.

Mutaka ya shiga gasar neman kyautuka da dama, inda ya lashe kambun Gwarzon Mai Barkwanci na Uganda a 2024, da gasar Source of the Nile Awards (SONEA) da wata kyautar daga Firaministan Uganda Busoga Kingdom.

Ya shawarci matasa da suke son fara yi bidiyo ko wallafa abu a intanet: “Ku san abin da kuke yi kuma ku jajirce. Ku dauki abin da kuke da sha’awa kuma a dabi’arku kuke son yinsa sannan ku yi ta yi.”

TRT Afrika da abokan hulda