Sa'idu Umar na Jam'iyyar PDP a Sokoto na kalubalantar nasarar Ahmed Aliyu na APC.

Kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da korafin da dan takarar PDP zaben gwamnan Sokoto Sa'idu Umar Ubandoma ya shigar gabanta inda yake kalubalantar nasarar Ahmad Aliyu na APC.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Huruna Mshelia sun yi watsi da korafe-korafen inda suka ce wanda ya shigar da karar ya kasa kawo kwararan hujjoji wadanda za su iya gamsar da kotu.

A watan Maris ne hukumar INEC ta ayyana Gwamna Ahmad Aliyu na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, sai dai Sa’idu Umar Ubandoma na Jam’iyyar PDP ya kai kara kotu kan zargin tafka almundahana a zaben.

A zaben, Ahmed Aliyu ya samu kuri'u 456,661, sai Sa'idu Umar Ubandoma na Jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 404,632.

Jihar Taraba

Haka zalika a Jihar Taraba Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta tabbatar da Agbu Kefas a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a G.A. Sunmonu sun yi watsi da karar da Farfesa Sani Yahaya na NNPP ya shigar.

Tun da safiyar Asabar aka saka jami'an tsaro a harabar kotun saboda dalilai na tsaro.

A yayin zaben da aka gudanar a watan Maris, Agbu Kefas na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 257,926 sai kuma Farfesa Sani Yahaya na NNPP ya samu kuri’u 202,277.

TRT Afrika