| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Nijeriya za ta karɓo bashin dala miliyan 618 domin sayen jiragen yaƙi shida
Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da karɓo bashin kusan dala miliyan 618 domin sayen jiragen yaƙi na ƙasar Italiya ƙirar M-346 da kuma wasu makamai.
Nijeriya za ta karɓo bashin dala miliyan 618 domin sayen jiragen yaƙi shida
Nijeriya na ƙara adadin kuɗin da take kashewa kan tsaro a 'yan shekarun nan a daidai lokacin da take fama da matsalolin tsaro. / Hoto: NAF / Others
24 Oktoba 2024

Majalisar Zartarwar ta Tarayya ta amince da karɓo bashin kusan dala miliyan 618 domin sayen jiragen yaƙi na ƙasar Italiya ƙirar M-346 da kuma wasu makamai ga rundunar sojin saman ƙasar, kamar yadda ministan watsa labarai na ƙasar Mohammed Idris ya sanar a ranar Laraba.

A farkon watan nan, rundunar sojin saman ƙasar ta sanar da cewa za ta sayi jiragen yaƙi 24 ƙirar M-346 da kuma jirgi mai saukar ungulu 10 ƙirar AW109 a shirin rundunar na sabunta jiragen yaƙinta.

Ana sa ran kai jiragen uku na farko ƙirar M-346 a farkon shekarar 2025 sai kuma sauran da suka rage a kai su ƙasar a tsakiyar shekarar 2026, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.

Nijeriya na ƙara adadin kuɗin da take kashewa kan tsaro a 'yan shekarun nan a daidai lokacin da take fama da matsalolin tsaro waɗanda suka haɗa da 'yan fashin daji a arewa maso yammacin ƙasar da kuma yaƙi da 'yan Boko Haram wanda aka shafe shekara aƙalla 15 ana gwabzawa a arewa maso gabas.

MAJIYA:TRT Afrika