| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Sama da mutum 30 sun rasu a Mogadishu bayan wani harin ƙunar-baƙin-wake
Jim kaɗan bayan harin ƙunar-baƙin-waken, sai wasu 'yan bindiga suka buɗe wuta kan farar hula waɗanda suke shaƙatawa a bakin teku inda aƙalla mutum 63 suka jikkata.
Sama da mutum 30 sun rasu a Mogadishu bayan wani harin ƙunar-baƙin-wake
Bam ɗin ya fashe ne a lokacin da mutane ke ninƙaya a bakin teku a Mogadishu. / Hoto: Reuters / Others
3 Agusta 2024

Aƙalla mutum 32 suka rasu da dama kuma suka samu raunuka bayan wani harin ƙunar-bakin-wake da kuma harin bindiga a Mogadishu babban birnin Somaliya, kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar a ranar Asabar.

"Sama da farar hula 32 suka rasu a wannan harin, kusan 63 kuma suka jikkata, wasu daga cikinsu suna cikin wani hali," kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda Abdifatah Adnan Hassan ya shaida wa manema labarai, inda ya bayyana ƙarin adadin waɗanda suka rasu daga bakwai.

Wani mai ƙunar-baƙin-wake ya tashi bam a ranar Juma'a da yamma a gefen Lido Beach -- wanda wuri ne da 'yan kasuwa da jami'ai kan je shaƙatawa, kafin 'yan bindiga suka far wa wurin, kamar yadda wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana.

"'Yan ta'addan marasa imani sun rinƙa harbin farar hula ba ƙaƙƙautawa," kamar yadda ɗan sanda Mohamed Omar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar.

"Jam'ian tsaron sun kawo ƙarshen ƙawanyar inda suka kashe duka 'yan bindigar biyar waɗanda suka kai hari kan farar hula da ke shaƙatawa a bakin teku," kamar yadda Omar ya bayyana.

Tuni 'yan ta'addan Al-Shabab suka ɗauki nauyin kai wannan hari.

Kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab ta sha kai munanan hare-hare a Somaliya a cikin 'yan shekarun nan.

MAJIYA:AFP