Turkiyya na da kudirin zama mai cin gashin kanta wajen amfani da makamashi/ Hoto: AA

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa an bude tare da kaddamar da cibiyar makamashin nukiliya ta Akkuyu irin ta ta farko a Turkiyya, tare da aika man nukiliya na farko zuwa cibiyar.

A yayin bikin kaddamar da cibiyar da Shugaba Erdogan da takwaransa na Rasha Putin suka yi ta hanyar sadarwar bidiyo, Erdogan ya ce ”Tare da aika man nukiliya ta sama da ta ruwa zuwa ga cibiyarmu ta Akkuyu, a yanzu Akkuyu ta samu matsayin zama cibiyar Nukiliya.”

Ya ce ”A yanzu Turkiyya ta shiga jerin kasashen duniya da ke da nukiliya, duk da jinkirin shekara 60 da aka samu.”

A watan Mayun 2010 ne hukumomin Turkiyya da na Rasha suka sanya hannu kan hada kai wajen kafa cibiyar nukiliya ta Akkuyu a yankin Mersin na Turkiyya.

A watan Afrilun 2018 aka kaddamar da fara aikin.

Ya kara da cewa “A shekarar da ta gabata Hukumar Tarayyar Turai ta amince da makamashin Nukiliya a matsayin mai tsafta tare da watsi da kokonto game da shi. Tare da Akkuyu, mun sanya kasarmu a jerin masu wannan cigaba.”

Shugaba Erdogan ya ci gaba da cewa “Kamar sauran ayyuka muhimmai, an samar da Akkuyu da kudaden da ba za su dora wani nauyi a kan kasafin kudinmu ba. Akkuyu ce aikinmu mafi girma na hadin gwiwa da Rasha.”

Erdogan ya kuma ce aikin da zai bayar da gudunmowa wajen rage sayo albarkatun gas da Turkiyya ke yi daga kasashen waje da dala biliyan 1.5 a kowacce shekara, zai kuma habaka kudin shiga da kasar ke samu.

Ya ce “Duba da yadda muka nazarci wannan aiki, nan da wani dan lokaci za mu fara aikin samar da wasu cibiyoyin na nukiliya a yankunan kasarmu daban-daban.”

Ana sa ran cibiyar makamashin nukiliya ta Akkuyu za ta dinga samar da makamashi na megawat 4,800, kuma manyan masarrafai hudu za su fara samar da lantarki a karshen wannan shekarar.

Erdogan ya kuma shaida cewa “Yadda girgiizar kasar 6 ga Fabrairu ba ta lalata aikinmu na Akkuyu ba, hakan ya bayyana kwarewar injiniyoyinmu da sauran ma’aikatan da suka samar da cibiyar.”

Shugaban na Turkiyya ya kuma taya murna ga dukkan ma’aikatan Turkiyya da na Rasha da suka gudanar da wannan aikin.

Putin ya yaba kaddamar da aikin

Shugaban kasar Rasha Vldimir Putin ya yaba da kaddamar da cibiyar Akkuyu inda ya bayyana ta a matsayin “aikin da zai kara dankon zumunci da hadin kai tsakanin bangarorin biyu.”

Putin ya ce “Wannan kaddamar da aiki ne da zai kawo amfanin tattalin arziki ga dukkan bangarorin biyu, kuma zai taimaka wajen habaka hadin kai tsakanin kasashenmu.”

Ya ci gaba da cewa “Abu ne mai kyau” yadda Turkiyya ta shiga jerin kasashen da suka ci gaba wajen masana’antu da kere-kere, a lokacin da take bikin cikar ta shekara 100 da zama jumhuriyya.”

Putin ya kuma bayyana cewa Akkuyu ce cibiyar nukiliya mafi girma a duniya, kuma a kowacce rana mutum 30,000 ne za su dinga yin aiki a wajen.

Haka zalika ya ce, an gudanar da wannan aiki bisa ka’idojin da Hukumar Makamashi ta Kasa da Kasa ta shimfida.

Putin ya kuma jaddada kalaman Darakta Janar na hukumar, Rafael Grossi na cewar tsaro da ka’idojin da aka yi amfani da su wajen samar da Akkuyu ne mafiya inganci da zamanci a yau.

TRT World