Ana hasashen yawan masu arzikin Afrika zai karu da kashi 65 nan da shekara 10.      .

Daga Sylvia Chebet

Ratar da ke tsakanin masu arziki da talakawa matsala ce ta duniya baki daya, duk da jita-jita ta asalin kididdigar yawa. Sai dai akwai alama hasashen masu kididdiga zai kara fito da fahimtar mutane fili.

A rahoton masu arzikin Afrika na bana, ya nuna cewa a yanzu haka akwai masu dimbin arziki a nahiyar guda 135,200 da ake kira high net-worth individuals ko kuma a takaice da HNWI, inda suke da arzikin dala miliyan ɗaya ko sama da haka da suke rayuwa a Afrika, baya da ’yan nahiyar guda 342 da suke da akalla dala miliyan 100 ko sama da haka, da kuma guda 21 da suke da arzikin akalla Dala biliyan 1 ko sama da haka.

Binciken ya kunshi akalla kasuwanni biyar da suka bayyana ainihin yadda arzikin nahiyar yake.

Giwaye biyar na Afrika

Kasashe biyar ne kawai suke da kashi 56 na masu arzikin dalolin miliyan a nahiyar. “Wannan lamarin akwai ban mamaki kasancewar akwai kasashe 54 a Afrika, amma a ce biyar daga cikinsu ne ke rike da sama da rabin arzikin nahiyar,” in ji Andrew Amoils, shugaban sashen bincike na New World Wealth a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Idan aka ce mutum ya shiga cikin mutanen da ake kira HNWI, yana da akalla Dala miliyan 1 da yake juyawa, wanda ya kunshi kamfanoni da hannun jari da tsabar kudi. Amoils ya ce, “Aiki ne babba mutum ya kai ga cikin wannan matakin.”

Duk da kalubalen da Afirka ta Kudu ta fuskanta a shekara goma da suka gabata, inda aka samu ragowar masu arziki a kasar da kashi 20, har yanzu kasar ce take kan gaba, inda ta ninka duk wata kasa yawan masu arzikin da suke kai matakin HNWI a nahiyar.

Kamar yadda sabon kididdigar ta nuna, Afirka ta Kudu na da masu arzikin da suka kai Dala biliyan guda biyar, masu akalla Dala miliyan 100 ko sama guda 102, sai masu miliyoyin Dala guda 37,400.

Yadda ake kara samun yawan masu arzikin, haka ratar da ke tsakaninsu da talakawa ke kara fadada, in ji masana. Hoto: Others

Kasar Masar ce ta biyu, inda take da masu akalla Dala biliyan guda bakwai, da masu akalla Dala miliyan 100 guda 52, da masu miliyoyin Dala guda 15,600.

Ta uku ita ce Nijeriya, wadda take da masu arzikin da suka taka matakin HNWI guda 8,200, sai Kenya ke biye mata da mutum 7,200, sannan Maroko mai mutum 6,800.

A tsakanin birane kuma, birnin Johannesburg ta Afrika ta Kudu ne ya fi tara masu arziki a nahiyar, inda akwai masu arzikin miliyoyin daloli 12,300 a cikinsa, sai masu akalla daloli miliyan 100 guda 25, sai masu akalla Dala biliyan guda biyu.

Birni na biyu shi ne Cape Town, shi ma a Afirka ta Kudu, inda a ciki akwai masu arzikin miliyoyin daloli guda 7,400, masu akalla miliyan 100 guda 28, sai mai arzikin akalla biliyan guda daya.

Birnin Cairo yana da yawan masu arziki guda 7,200, sai Nairobi mai mutum 4,400, sai Legas mai masu arziki 4,200.

A cewar Amoils, kasashen da suka fi yawan masu arzikin da suka kai matakin HNWI, suna kuma da matsakaita masu arziki. “Akwai alaka tsakanin manyan masu arziki da matsakaita masu arziki,” in ji shi.

Sannan ya kara da cewa, “Idan kana da masu arziki, yawancinsu za su kasance ’yan kasuwa ne don haka za su dauki wasu mutanen aiki.”

A daya bangaren kuma, idan kasa ba ta da masu arziki da yawa, “to ko dai matalauciyar kasa ce, ko kuma gwamnati ce ke rike da mafi yawan arzikin kasar.”

Masu arzikin miliyoyin daloli

A duniya akwai ’yan asalin Afrika guda 54 da suke da arzikin akalla dala biliyan, amma guda 21 ne kadai suke zaune a nahiyar.

Wani binciken mai ban mamaki shi ne wasu kasashen suna da manyan masu arziki mazauna kasar, sama da wadanda aka haifa a kasar. Misali, kasar Maroko wadda ke da masu arzikin akalla dala biliyan 1 guda 25, amma kadan daga cikinsu ne aka haifa a kasar.

Wanda ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, wanda a Afirka ta Kudu aka haife shi, yanzu yana da arzikin Dala biliyan 193.0, yana cikin wadanda suka bar nahiyar, suka koma Amurka da zama.

“Idan wani mai karbar albashin miliyoyin daloli a shekara ya bar wata kasa, za a iya maye gurbinsa. Amma idan dan kasuwa ne mai wani babban kamfani ya bar kasar, sannan ya tafi da kasuwancinsa, wannan yana da illa sosai,” inji Amoils.

Idan suka fice daga kasa, suna barin gibin aiki da samar da arziki a kasar. “Duk inda suka je, damarmakin na binsu ne,” inji Chidinma Okebalama, daya daga cikin masanan da suka gudanar da binciken.

Yadda masu arziki ke ficewa daga Nijeriya

Kamar yadda rahoton New World Wealth ya nuna, kusan masu arzikin da suka kai matakin HNWI 300 ne suke barin Nijeriya duk shekara a sama da shekara biyar da suka gabata.

Amoils ya ce a shekara goma baya, Nijeriya ta kusa ninka Kenya yawan masu arziki, amma yanzu kusan kan-kan-kan suke. “Bayan ficewar da masu arzikin suke yi, akwai kuma faduwar darajar Naira, inda ta karye da kusan kashi 80 idan aka kwatanta da Dalar Amurka,” in ji shi.

Kudin Nijeriya, wato Naira ta sha fama da karyewar daraja kafin ta fara farfadowa a kwanan nan. Hoto: TRT Afrika

A watan Fabrairun bana ne Naira ta yi faduwar ban mamaki, inda ta kai Naira 1,900 a kan Dala 1, amma yanzu ta farfado da kashi 40 a cikin ’yan makonnin nan.

“Ita ma kasar Kenya darajar kudinta ya fadi, amma ba kamar Nijeriya ba,” inji Amoils.

“Masu arziki sun fice daga Kenya ma, amma kadan, ba kamar Nijeriya da Afirka ta Kudu da Masar ba.”

A shekarun baya, adadin masu arzikin kasar Kenya sun ragu daga 8,500 zuwa 7,200. Har yanzu a kasar babu wanda arzikinsa ya kai Dala biliyan, ita kuma Nijeriya tana da uku.

Sabuwar kididdiga na nuna cewa kusan masu arzikin da suka kai matakin HNWI guda 18,700 suke fice daga nahiyar a shekara goma da suka gabata, inda suka koma wasu yankuna na duniya da kasuwanci ya fi ci.

Masu arziki na karuwa a Mauritus

Mauritius, wadda take ta shida a cikin kasashen da suka fi arziki a nahiyar Afrika, ita ce ta fi samun karuwar masu arziki a shekara goma da suka gabata, inda adadin masu arzikin da suka kai matakin HNWI ya karu daga kusan 2,800 a shekara goma da suka gabata, zuwa 5,000.

“Wannan bai rasa nasaba da cigaban tattalin arzikin kasar, da kuma yadda masu arziki suke komawa cikinta. Masu arziki da dama sun koma kasar da harkokinsu,” kamar yadda Amoils ya bayyana wa TRT Afrika.

Haka kuma akwai saukin haraji a kasar, da kuma ingantacciyar dimokuradiyya, wadanda duk suna cikin abubuwan da masu zuba jari na duniya suke dubawa.

Ana hasashen kasar Mauritus za ta samu karuwar masu arziki da kashi 95, wanda hakan zai saka ta a cikin kasashen duniya masu fuskantar karuwar arziki. Ita ma Namibia ana mata wannan kallon, inda ake hasashen masu arzikinta za su karu da kashi 85 a shekarar 2033.

Mafi yawan ’yan Afrika suna rayuwa a kasa da Dala biyu ne a kullum. Hoto: Reuters

Sauran kasashen da ake hasashen masu arzikinsu za su karu da kashi 80 ko sama da haka nan da shekara 10 sun hada da Maroko da Zambiya da Kenya da Uganda da Rwanda.

Karuwar masu arziki a gaba

Jarin da ke nahiyar Afrika a yanzu ya kai Dala triliyan 2.5, sannan ana hasashen masu arzikin miliyoyin dalolinta za su karu da kashi 65 nan da shekara 10, kamar yadda binciken ya nuna.

“Muna sa ran samun karuwar masu arziki a wasu bangarori irin su fasahar zamani dad a kasuwancin zamani da yawon bude ido da hako ma’adinai da nishadi da kafofin sadarwa da sauransu,” in ji Amoils.

Amma tsaikon da ake samu na mulki da karyewar darajar kudi da haraji za su iya kawo tsaiko.

A Afirka ta Kudu, bangaren harkokin kudi ne suke kan gaba wajen damar samar da masu arziki.

“Kusan kashi 40 na masu arzikin da za a samu daga Afrika ta Kudu daga wannan bangaren za su fito. Yawancin masu arzikin Afirka ta Kudu ko dai lauyoyi ne ko masana harkokin kudi,” in ji Amoils.

A bangaren birane kuwa, ana hasashen nan da shekarar 2030, birnin Cape Town zai dara birnin Johannensburg wajen tara masu arziki na Afrika.

Masana suna hasashen birnin Kigali na Rwanda da Windhoek da Swakopmund na Namibia, da Tangier da Marrakech na Maroko za su samu karuwar masu arziki da kashi 85 na da shekara 10.

TRT Afrika