Babban Bankin Nijeriya ya sha nanata gargadi kan muzanta Naira. / Photo: Getty Images

Daga Abdulwasiu Hassan

Tun daga zaratan mawakan Gabas ta Tsakiya, zuwa da masu rawa na Mariachi na Mexico da ke sanya ƙatuwar malafa, ƴan rawa da mawaka a al'adu daban-daban na duniya na samun kyaututtuka ta hanyar lika musu tsabar kudi a yyin da suke tsaka da cashewa.

A wuraren bukukuwa na Nijeriya, musamman tarukan musamman, ba bakon abu ba ne ka ga ana ta watsa takardun Naira ga mawakan da aka dakko don cashewa a wajen, ko ma a kan mahalarta taron da suke taka rawa.

Wasu masu kudin ma, a wasu lokutan ba Naira suke watsawa ba, har ma da kudaden waje na dala da yuro.

Ana yi wa wannan abu kallon ba komai a al'adance da yanayin zamantakewa, sai dai idan mutane suka dinga taka kudin da kafafuwansu, wannan ne abin da ba a yarda da shi.

A Nijeriya, wannan al'ada ce da ake gani a wajen bukukuwa, duk da gargadi da kiran da Babban Bankin kasar ke yi na a daina muzanta Naira.

Abinda ba a tsammata ba ya faru. yunkurin daukan matakin ba sani ba sabo daga Hukumar EFCC, ciki har d misalin gurfanarwa da daure shahararre, wanda hakan ya janyo cece-ku-ce daga dukkan bangarori.

Haka zalika wani mai yawan mabiya a shafukan sadarwa na zamani ya gurfana a gaban kotu saboda wannan laifi da aka zage shi da aikatawa. Sai da ya biya Naira miliyan 10 don belin kansa.

Tsoron tsattsauran hukunci

Matakin da EFCC ta dauka na hukunta sansannun mutane ya sanya tsoro a zukatan sauran jama'a kan me zai je ya komo.

"Ba na wulaƙanta kudade," in ji wani shahararren mawakin Nijeriya da ya fitar da wani sakon bidiyo, yana mai tunatar da yadda yake raba kudade ga mabukata a unguwannin talakawa.

"Muna taimakon mutane da yawa, musamman wadanda ke unguwannin talakawa. Idan ka gan ni ina watsa kudade, to ina rokon ka yafe min. Ina raba wa mutane kudi ne kawai."

An dinga yada bidiyon da yake bayanin matsayarsa a lokacinda ya ziyarci yankin Yarbawa baya-bayan nan.

"Magoya bayana, idan kun ga ban watsa kudi a kwanakin nan ba, ku sani cewa bayan Ubangiji, akwai gwamnati, idan batu na kudi ne, ku bude asusu, sai na dinga tura muku asusunku," ya fada w amagoya bayansa.

Kama masu muzanta Naira da hukumar yaki da cin hanci ke yi ba ya tsaya ga mashahuran mutane kawai ba ne. 'Yan kasa gama-gari sun ankare ne tare da yin kaffa-kaffa kan kar a kama su suna aikata abin da ba da jimawa ba yake matsayin nuna isa.

"A karan kaina, ba na son watsa kudade ga jama'a. Ina yin hakan ne kawai a wasu lokutan a matsayin wani bangare na al'adar nuna yabawa ga mai waka ko mai yin rawa," in wata mace 'yar Nijeriya da ta nemi a boye sunanta.

"Ina jin hakan na zama wani bangare na taka rawata tare da mai yin biki, ya danganta da taron d aake yi," in ji ta yayin tattaunawa da TRT Afirka.

A gefe guda kuma, ta yi amanna da cewar daukar matakan ba sani ba sabo kan yin likin kudaden a wajen bukukuwa "Zai taimaka wajen dakile almubazarranci da ake gan a wajen bukukuwa."

"Ina zargin mafi yawancin mutane na yin hakan ne kawai don nuna inda suka nufa, duk da cewa da yawansu ba su da karfin yin hakan. Wasu ma rantar kudin suke yi. Na sha ganin mutane na cizon yatsa bayan sun yi yi likin kudade a wajen biki." in ji matar.

Abinda doka ke cewa

Buhari Yusuf, wani lauya, ya ce Naira kudi ne da ake amfani da shi mallakar Tarayyar Nijeriya kuma Babban Banki yake kula da ita.

Ya fada wa TRT Afira cawa "A matsayin mi kula da kudade, gwamnati na da hurumin gurfanar da duk wanda aka samu da laifin cin zarafin kudin kasa. Mutane na da mallakin darajar kudin da ke hannunsu ne kadai."

Duk da cewa abin da ake nufi da "cin zarafin Naira" ya danganta da yadda kowa yake kallon sa, amma duk wanda aka kama da laifin na iya fuskantar dauri har na tsawon watanni shida, tarar Naira 50,000 ko dukka biyun.

Buhari ya ce "Za a iya gaza kama mutum ne kawia idan har ba a iya samun lambaobin kudaden da ake zargin an ci zarafin nasu ba."

Masu nazari na cewa wadanda z asu ci gaba da aikata al'adar bayar da kyautar Naira ga mawaka a wajen bukukuwa, ya zama dole su kula sosai kan yadda za su yi ta'ammali da kudin Nijeriya.

Buhari ya bayar da shawarar cewa "Akalla ku tabatar da ba ku jefar da kudin a kasa wani ya taka da kafarsa ba."

TRT Afrika