Kenya ta sake jinkirta harba tauraron dan Adam dinta na nazari zuwa sararin samaniya a karo na uku cikin mako guda.
A ranar Juma’a, kamfanin SpaceX da ke jan ragamar shirin harba tauraron dan adam din mai suna Taifa 1, ya fasa harbawa tauraron ‘yan dakiku kafin harba shi saboda rashin kyawun yanayi.
"An ba da umarnin dakatarwar ne saboda rashin kyawun yanayi...kumbon da tauraron suna lafiya," in ji SpaceX.
Yunkuri na hudu wanda kamfanin SpaceX ya bayyana a matsayin "damarmu ta harba tauraron nan gaba" za a yi shi a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu ta rokar hanyar Falcon 9.
Hukumar Sararin Samaniya ta Kenya ta ce tauraron dan adam din zai dauki hotuna don sa ido kan yanayi da ambaliyar ruwa da noma da albarkatun kasa da kuma sauyin yanyi.
Injiniyoyi tara ‘yan Kenya ne suka tsara tare da hada tauraron wanda ya ci kudi kimanin dala 370,000.
An jinkirta harba tauraron dan adam din Turkiyya ma
A farkon makon nan aka dakatar da harba tauraron dan Adam din Turkiyya sau biyu saboda rashin kyawun yanayi.
SpaceX ya ba da sanarwar cewar an jingina harba tauraron dan adam din Turkiyya mai daukar hoto mai matukar kyau da aka fara hadawa a karon farko a kasar, saboda rashin kyawun yanayi.
An yi niyyar harba tauraron dan adam din da aka yi Turkiyya mai suna IMECE, cikin sararin samaniya da safiyar Juma’a daga barikin sojin sama na Vandenberg a jihar California ta Amurka, da misalin karfe 06: 48 agogon GMT kafin a jinkirta harbawan.
A halin yanzu an shirya harba IMECE da misalin karfe 06.47 agogon GMT ranar Asabar, 14 ga watan Afrilu, kamar yadda SpaceX mai jagorantar aikin ya bayyana a shafinsa na Twitter ranar Juma’a.
Da zarar an harba shi sararin samaniya, tauraron IMECE zai yi amfani ta hanyar sa ido a fannin tsaro da muhalli da kiyaye aukuwar bala’i da duba fadadar birane da noma da kuma harkokin daji.

















