Ɗaruruwan Falasɗinawa sun yi zanga-zanga a birnin Ramallah don neman ƙasashen Musulmai su tura sojoji don taimaka wa Falasɗinawa a Gaza  ranar 24 ga watan Mayu, 2024. [Reuters/Ammar Awad]

Ɗaruruwan Falasɗinawa sun yi zanga-zanga ranar Juma'a a kan titunan birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda suka yi kira ga ƙasashen Musulmai su ba su taimakon sojoji domin tunkurar hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.

Masu zanga-zangar suna riƙe da kwalaye da tutoci da ke kira ga ƙasashen Musulmai su ɗauki matakan soji domin samar da 'yanci ga yankunan Falasɗinu.

Masu gangamin sun yi kira ga ƙasashen Musulmai irin su Masar, Turkiyya, Saudiyya, Aljeriya da sauran ƙasashen Musulmai su taimaka don kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi a yankin Gaza.

Kazalika a ranar ta Juma'a, wasu ƙungiyoyin Isra'ilawa da 'yan ƙasashen waje sun sanya wa kawunansu sasari suka haɗa jikinsu da ƙofar shiga ofishin Amurka da ke lura da Lamuran Falasɗinawa a Birnin Ƙudus don bijire wa yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.

Masu fafutuka sun ce 'yan sanda sun kama masu zanga-zangar guda bakwai cikin gomman da suka taru a wurin.

Wasu bidiyoyi da aka wallafa a soshiyal midiya sun nuna yadda 'yan sanda suka riƙa amfani da ƙarfi wajen ture masu zanga-zangar. Kawo yanzu rundunar 'yan sandan yankin ba ta ce uffan ba game da zargin da aka yi wa jami'anta na gallaza wa masu zanga-zangar.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren kisan kiyashi a Gaza tun watan Oktoban da ya wuce, duk da ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi wanda ya buƙaci ta tsagaita nan-take a Gaza.

Ta kwashe fiye da wata bakwai tana luguden wuta a yankin inda ta lalata gine-gine da hana shigar da kayan agaji da suka haɗa da abinci da magunguna da samar da ruwan sha.

Kawo yanzu dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa sama da 35,800, galibinsu mata da yara, tare da jikkata sama da mutum 80,200.

TRT World