| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Kotun Kolin Guinea ta tabbatar da Doumbouya a matsayin wanda ya lashe zaben kasar
An gudanar da zaben naranar 28 ga Disamba a karkashin sabon kundin tsarin mulki da ya kawar da dokar hana tsaffin sojoji yin takara, ya kuma kara wa’adin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai.
Kotun Kolin Guinea ta tabbatar da Doumbouya a matsayin wanda ya lashe zaben kasar
Shugaba Doumbouya ya samu sabon wa'adi na shekaru bakwai. / Reuters
5 Janairu 2026

Kotun Koli a Guinea a ranar Lahadi ta tabbatar da nasarar zaben Janar Mamadi Doumbouya, wanda hakan ya tabbatar da sauyin shugaban soji zuwa shugaban da aka “zaba” shekaru hudu bayan ya yi juyin mulki a kasar da ke Yammacin Afirka.

Doumbouya ya lashe zaben farko a kasar tun bayan juyin mulkin 2021 bayan ya samu kashi 86.7 cikin 100 na kuri'un da aka kada, a cewar Babban Daraktan Zabe. Kuma da ma masu sharhi sun yi hasashen samun wannan nasara da Kotun Koli ta tabbatar a babban birnin Conakry.

"A yau, babu wanda ya yi nasara ko wanda ya sha kaye. Akwai kasar Guinea daya kawai, wacce aka hade kuma ba za a iya raba ta ba," in ji Doumbouya a wani jawabi da aka watsa a daren Lahadi, yana kira ga 'yan kasar da su "gina sabuwar Guinea, Guinea mai zaman lafiya, adalci, wadata ga kowa, da kuma cikakken ikon siyasa da tattalin arziki."

Yero Baldé, wanda ya zo na biyu da kashi 6.59 cikin 100 na kuri'un, ya shigar da kara yana zargin hukumar zabe da yin amfani da sakamakon don goyon bayan Doumbouya. Amma hukumomi sun ce ya janye karar kwana daya kafin hukuncin Kotun Kolin.

Karin wa’adin mulki

An gudanar da zaben naranar 28 ga Disamba a karkashin sabon kundin tsarin mulki da ya kawar da dokar hana tsaffin sojoji yin takara, ya kuma kara wa’adin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai.

Masu suka sun ce Doumbouya ya murkushe abokan hamayyar siyasa da masu adawa tun bayan juyin mulkin 2021, wanda ya bar shi babu wani babban ɗan adawa a tsakanin sauran 'yan takara takwas da ke takarar.

'Yan adawar da aka raunata "sun mayar da hankali kan Mamadi Doumbouya a matsayin mutum ɗaya tilo da zai iya tabbatar da ci gaban siyasra kasar," in ji N'Faly Guilavogui, wani mai sharhi kan harkokin siyasa na Guinea.

"'Yan Guinea suna jiran ganin irin ƙoƙarin da zai yi don tabbatar da zaman lafiya da sulhu a siyasance," in ji Guilavogui.

Duk da albarkatun ma'adinai masu yawa na ƙasar, ciki har da kasancewar ta babbar mai fitar da bauxite da ake amfani da shi don yin aluminum, fiye da rabin mutanenta miliyan 15 suna fuskantar matsanancin talauci da rashin isasshen abinci, a cewar Hukumar Abinci ta Duniya.

Babban shirin gwamnati mafi mahimmanci shi ne aikin haƙar ma'adinai a Simandou, babbar matattarar ma'adinan ƙarfe a duniya.

Aikin da China ke mallakar kashi 75 cikin 100 ya fara ne a watan Disamba bayan shekaru da dama da aka yi ana jinkiri.