‘Yan sanda a ƙasashe 16 na Afirka sun kama mutum 651 a makonnin baya-bayan nan, inda suka tarwatsa wata babbar ƙungiyar masu aikata laifuka ta intanet inda waɗanda ake zargin suka karɓe miliyoyin daloli daga hannun waɗanda suka yaudara, kamar yadda ‘yan sandan ƙasa da ƙasa na Interpol suka sanar a ranar Alhamis.
Aikin wanda da ya ɗauki tsawon makonni takwas, ya rusa wata hanyar sadarwa da ta damfari fiye da dala miliyan 45 daga ɗaruruwan mutane, watakila ma dubbai — mafi yawansu a Afirka — in ji hukumar ‘yan sandan ta Interpol.
Rahotanni sun ce damfarar ta intanet ta shafi yaudara ta hanyar zuba jari da damfara ta kuɗin waya, da damfara ta hanyar manhajoji na bogi.
Masu bincike sun kuma ƙwace na’urori 2,341 tare da rufe jerin adireshin intanet waɗanda masu yaudarar ke amfani da su wurin gudanar da laifuka, in ji ‘yansandan na Interpol.
‘Yansandan sun ce sun kai samamen ne kan waɗanda ake zargi a tsakanin watan Disamba zuwa Janairu.
“Waɗannan ƙungiyoyin masu aikata laifukan ta intanet sun jawo babbar asara ta kuɗi ga mutane da kasuwanci da al’umma baki ɗaya ta hanyar alƙawura na ƙarya,” in ji Neal Jetton, shugaban sashen yaki da laifukan yanar gizo na Interpol.
“Ina karfafa gwiwar duk wanda aka yaudara ta hanyar intanet da ya kai kukansa ga jami’an tsaro,” in ji shi.
Ƙasashen da suka shiga wannan aiki sun haɗa da Angola, Benin, Kamaru, Chadi, Gabon, Gambiya, Ghana, Ivory Coast, Kenya, Namibia, Nijeriya, Rwanda, Senegal, Uganda, Zambia da Zimbabwe.







