Dakarun RSF sun ƙaddamar da hare-haren da sanyin safiyar ranar Juma’a a wasu wurare a birnin Omdurman na Jihar Khartoum da kuma birnin Atbara na Jihar River Nile, kamar yadda kafofin watsa labaran cikin ƙasar Sudan suka ruwaito.
Hare-haren na baya bayan nan na zuwa ne sa’o’i bayan RSF ta ce ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta masu shiga tsakani da Amurka ke jagoranta suka gabatar.
Mazauna biranen biyu sun ba da rahoton cewa sun ji ƙarar fashewa da kuma ƙarar bindigogin kakkaɓo jiragen sama da aka harba da sanyin safiya yayin da sojojin Sudan suka mayar da martani da jirage mara matuƙi, in ji kafar watsa labaran Sudan ta Sudan News.
Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutane da ko kuma kadarorin da aka lalata sakamakon hare-haren ba, kuma sojin ƙasar da rundunar RSF ba su fitar da sanarwa game da hare-haren ba.
Bayan rundunar RSF ta kama Al Fasher, wuri na ƙarshe da ke hannun rundunar sojin a yammacin Darfur ƙasa da mako biyu da suka wuce, da alama rundunar tana mayar da hankalinta zuwa gabashi ta Khartoum da kuma yankin Kordofan mai arziƙin mai.
Khartoum ya ɗan samu kwanciyar hankali tun lokacin da sojin Sudan suka sake karɓe iko da shi a wannan shekarar, amma rundunar RSF ta ci gaba da kai hare-hare kan wasu yankuna inda take kai hari kan sansanonin soji da wuraren fararen-hula.
Wani mazaunin Omdurman, wani yanki na Khartoum, ya shiada wa AFP bisa sharaɗin sakaya sunansa domin tsoron ramuwar gayya, cewa an tayar da su da "misalin ƙarfe 2 na dare (ƙarfe 12 na dare agogon GMT) da ƙarar abubuwa masu fashewa kusa da sansanin sojin Wadi Sayidna ".
Wani mazaunin garin kuma ya bayyana cewa sun "ji jirage mara matuƙa a sama da misalin ƙarfe huɗu na dare kafin fashewar wani abu da ya afka wa " wata tashar wutar lantarki da ke kusa, lamarin da ya janyo ɗauke wuta a yankin.
A Atbara inda soji ke da iko, wanda ke da nisan kimanin kilomita 300 arewa da Khartoum, wani mazaunin garin ya bayyana cewa wasu jirage mara matuƙa "sun bayyana a saman birnin jikm ƙadan bayan ƙarfe uku na dare " ranar Juma’a.
"Bindigogin kakkaɓo jiragen sama sun kakkaɓo daga sama, amma na ga gobara ta ɓarke kuma sun ji sautin fashewra abubuwa a gabashin birnin," in ji mazaunin garin, wanda shi ya yi bayani bisa sharaɗi na sakaya sunansa bisa dalilai na tsaro.
Wani mazaunin garin na Atbara kuma ya ce: "Na ga jirage mara matuƙa goma a saman birnin, kuma bindigogin kakkaɓe jiragen sama sun ci gaba da kakkaɓo su ɗaya bayan ɗaya, sai dai kuma a lokaci ɗaya na ga gobara a gabashin birnin."
Babu rahoto nan-take game da adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su, kuma sojin da kuma RSF ba su yi tsokaci a kan hare-haren ba kawo yanzu.
A halin yanzu, ƙungiyar likitocin Sudan ta ce RSF ta yi luguden wuta kan wani asibiti a birnin Dilling da ke South Kordofan da aka yi wa ƙawanya ranar Alhamis, lamarin da jikkata wasu marasa lafiya.
Luguden wutan "ya lalata ɓangarorin ɗaukar hoton ƙasusuwa da sauran sassan jiki ", lamarin da ya durƙusar da ɗaya daga cikin muhimman wuraren jinyar yankin, in ji ƙungiyar.
Tun watan Yunin shekarar 2023 ne dai Dilling ya kasance ƙarƙashin ƙawanyar RSF.












