| Hausa
DUNIYA
9 MINTI KARATU
Yara na cikin hadari saboda ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa asibitocin Gaza
Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Yara na cikin hadari saboda ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa asibitocin Gaza
Yara na cikin hadari saboda ƙwanyar da Isra'ila ta yi wa asibitocin Gaza. Hoto: Reuters / Reuters

1730 GMT - Malaman addini na Indonesiya sun fitar da fatawar kaurace wa kamfanoni masu alaƙa da Isra'ila

Majalisar Ƙoli ta Malaman Addinin Musulunci ta kasar Indonesiya ta fitar da wata doka a yau Juma’a inda ta bukaci a kaurace wa kayayyaki da kuma ayyuka daga kamfanonin da ke goyon bayan Isra’ila domin nuna goyon bayan Falasdinawa.

Fatawar da Majalisar Malaman Indonesiyan, MUI ta fitar ta ce dole Musulman ƙasar su nuna goyon bayan Falasɗinawa kan "cin zalin da Isra'ila ke musu", a yayin da ta kuma ayyana cewa goyon bayan Isra'ila da masu tallafa mata "haramun ne" ko kuma ya kauce wa dokar Musulunci.

Dokar ta (fatwa) da Majalisar Malamai ta Indonesiya ko MUI ta fitar, ta ce dole ne musulmin kasar su goyi bayan gwagwarmayar Palasdinawa da "zamantakar Isra'ila", tare da bayyana cewa goyon bayan Isra'ila ko magoya bayanta haramun ne, ko kuma adawa da Musulunci.

1230 GMT - Idan akwai wuta a doron duniya, to arewacin Gaza ne: MDD

Ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba za su iya kai motocin agaji zuwa arewacin Gaza ba yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi a yankunan da aka yi wa ƙawanya.

Kakakin ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya Jens Laerke ya shaida wa taron manema labarai na mako-mako a birnin Geneva cewa, "idan akwai wuta a duniya, to arewacin Gaza ne."

Laerke ya ce manyan motocin jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya sun isa kudancin Gaza, duk da haka, ba za su iya kai kayan agaji zuwa arewacin yankin da dubban daruruwan mutane ke zaune ba.

A baya-bayan nan ne wata tawagar ƙwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Falasdinawa na cikin “hadarin kisan kare dangi” yayin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da mamaye Gaza.

1300 GMT — Yara na cikin hadari saboda ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa asibitocin Gaza

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa sojojin Isra'ila sun killace asibitocin Al Rantisi da Al Nasr da ke tsakiyar Gaza.

Mai magana da yawun ma'aikatar Ashraf Al Qudra ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa yaran da ke jinya na cikin hatsari mai tsanani sakamakon killace asibitocin da sojojin Isra'ila suka yi.

Ya ƙara da cewa ma’aikatan lafiya da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a asibitocin biyu suna cikin ƙawanya ba tare da samun abinci da ruwa ba.

Tun da farko a ranar Juma'a, Ministan Lafiya na Falasdinu Mai Alkaila ya ce asibitoci 18 a Gaza sun daina aiki tun farkon harin da Isra'ila ta kai a farkon watan Oktoba.

1209 GMT — Dole a daina kashe-kashen da ake yi a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga a kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila, kamar yadda wani babban jami'in MDD ya faɗa.

"Hanyar da mahukuntan Isra'ila suke kai a halin yanzu ba za ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankalin da Isra'ilawa da Falasdinawan suke so kuma suka cancanci su samu ba," a cewar Philippe Lazzarini, shugabar Hukumar Kula da Ƴan gudun Hijirar Falasɗinu ta MDD (UNRWA), kamar yadda ta rubuta a wata maƙala ta ra'ayinta da aka wallafa.

"Rushe yankunan gaba ɗaya ba ita ce mafita ga munanan laifukan da Hamas ta aikata ba. Sabanin haka, tana samar da sabbin al’ummar Falasdinawan da ke cikin baƙin ciki, wadanda za su iya ci gaba da tashe-tashen hankula. Dole ne kawai a daina kashe-kashen."

11:30 GMT — An sake yin 'luguden wuta' a Asibitin Al Shifa na Gaza — WHO

Mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce "ana ta yin luguden wuta" a Asibitin Al Shifa, tana mai karawa da cewa asibitoci 20 sun daina aiki a Gaza.

Tun da farko, gwamnatin Hamas da ke Gaza ta ce wani hari da Isra'ila ta kai a babban asibitin yankin ya yi sanadin mutuwar mutum 13.

"Mutum goma sha uku sun yi shahada sannan gommai sun jikkata sakamakon hari ta sama da Isra'ila ta kai ginin Asibitin Al-Shifa a yau" a tsakiyar Birnin Gaza, a cewar sanarwar da gwamnati ta fitar.

Da aka tambaye ta kan harin da aka kai a harabar asibitin, kakakin WHO Margaret Harris ta ce: "Ban samu cikakken bayani kan Al Shifa ba amma muna sane cewa ana yi masa luguden wuta".

Ta kara da cewa ana "fafatawa mai zafi" a yankin, tana mai bayyana abubuwan da abokan aikinta da ke yankin suka gaya mata.

09:00 GMT — Turkiyya ta aika da jirgin ruwa cike da kayyakin jinkai da na kiwon lafiya zuwa Gaza

Turkiyya ta aika da kusan tan 500 na kayayyakin jinkai da na kiwon lafiya zuwa Gaza inda jirgin ruwan ya nufi iyakar Masar.

A safiyar ranar Juma’a ne jirgin ruwan Turkiyya ya tashi daga lardin Izmir dauke da kayan agaji don kai wa Falasdinawa da ke yankin Gaza da aka yi wa kawanya.

An loda kayayyakin agajin da motocin daukar marasa lafiya a cikin jirgin ruwa mai dakon kaya da ya tsaya a tashar ruwan Alsancak ta Izmir da yammacin ranar Alhamis.

Daga nan jirgin ya tashi zuwa Al Arish na kasar Masar, kusa da iyakar Rafah ya kasar da ke tsallaken yankin da ke fama da rikici.

07:30 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaza — Jami'ai

Kungiyar Bayar da Agaji ga Falasdinawa 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta ce an kashe ma'aikatanta 99 tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.

Kwamishina Janar na UNRWA Philippe Lazzarini ne ya bayyana haka a wurin taron Kasashen Duniya Don Samar Da Jinkai ga Fararen-Hulan Gaza da aka yi a Paris, babban birnin Faransa.

"Wata daya da ya gabata ya kasance mai matukar wahala ga UNRWA," in ji Lazzarini.

Ya ce "an kashe abokan aikina 99 maza da mata a Gaza. Wannan shi ne adadi mafi girma na ma'aikatan kungiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kashe sakamakon rikici a kankanen lokaci."

05:30 GMT — Yakin Isra'ila a Gaza ya jefa Falasdinawan Gaza 'sama da 400,000' cikin talauci

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda tattalin arzikin Falasdinu yake rushewa bayan Israila ta kwashe fiye da wata daya tana yi wa Gaza luguden wuta tare da yi wa daukacin yakin kawanya.

Tattalin arzikin Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza ya fadi da kashi hudu cikin dari lamarin da ya jefa fiye da mutum 400,000 cikin talauci — abin da ba a taba gani ba a yakin Syria da na Ukraine, da ma yake-yaken da aka yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na yankin Gaza a baya.

Isra'ila ta lalata ko ta rusa akalla kashi 45 cikin dari na dukkan gidajen Gaza, a cewar wata kididdiga da Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Ci-gaba UN Development Program da kuma na Tattali Arziki da Walwala a Yankin Asiya wato UN Economic and Social Commission for West Asia suka fitar.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda