| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Sojojin Sudan sun ƙwato wani muhimmin birni daga hannun rundunar RSF
Sojojin Sudan sun ce sun ƙwato birnin Sinja da ke kudancin Khartoum babban birnin ƙasar daga hannun rundunar RSF. Ko a kwanakin baya sai da sojojin Sudan suka ƙwace iko da wasu muhimman wurare kamar Jebel Moya da garuruwa kamar As-Suki da Ad-Dinder.
Sojojin Sudan sun ƙwato wani muhimmin birni daga hannun rundunar RSF
Rundunar sojin ta wallafa wani bidiyo wanda ke nuna sojojin ƙasar a cikin hedikwatar runduna ta 17 ta sojin ƙasa da ke Sinja. / Hoto: Reuters / Others
23 Nuwamba 2024

Rundunar Sojin Sudan a ranar Asabar ta sanar da sake kwato birnin Sinja, babban birnin jihar Sennar da ke kudu maso gabashin kasar daga hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF).

A wata gajeruwar sanarwar da ta fitar, ta bayyana cewa “An ƙwato birnin Sinja daga hannun dakarun RSF.”

Rundunar sojin ta wallafa wani bidiyo wanda ke nuna sojojin ƙasar a cikin hedikwatar runduna ta 17 ta sojin ƙasa da ke Sinja.

Haka kuma bidiyon ya nuna yadda mazauna Sinja ke murna bayan sojojin ƙasar sun ƙwace iko da birnin na Sinja.

Zuwa yanzu dai rundunar ta RSF ba ta fitar da sanarwa dangane da lamarin ba.

A ranar 24 ga watan Yuni, RSF ta kaddamar da farmaki a jihar Sennar, inda ta kwace garuruwa da dama ciki har da Sinja, wanda suka shiga a ranar 29 ga watan Yuni.

A baya-bayan nan dai sojojin Sudan sun samu ci gaba sosai a yankin Sennar, inda suka sake kwace iko da wasu muhimman wurare kamar Jebel Moya da garuruwa kamar As-Suki da Ad-Dinder.

Tun a tsakiyar watan Afrilun bara, sojojin Sudan da RSF suka shiga cikin rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 20,000 tare da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ana ta samun kiraye-kirayen daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa kan a kawo karshen rikicin, yayin da yakin ya jefa miliyoyin mutanen Sudan cikin halin yunwa da rasa rayuka sakamakon karancin abinci, inda fadan ya bazu zuwa jihohi 13 daga cikin 18 na Sudan.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Harin RSF na watan Oktoban 2025 a Al-Fasher na Sudan ya kashe aƙalla mutum 6,000: Rahoton MDD
AU: Shugabannin Afirka sun ƙaddamar da taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da batun ruwa da sauyin yanayi
Afirka ce kan-gaba wajen faɗaɗa samar da lantarki ta hasken rana a shekarar 2025: Rahoto
Gwamnatin Ghana ta ba da umarnin sarrafa kashi 50 cikin 100 na koko a cikin ƙasar
Sudan: Aƙalla mutum 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kogin Nilu
Kasashe shida sun shiga Kwamitin Tsaro na Tarayyar Afirka
RSF ta kashe ƙananan yara a harin da ta kai wani masallaci a yankin Kordofan na Sudan
Saudiyya ta yi tur da RSF kan munanan ayyukanta a Al Fasher, ta buƙaci a ba da hanyar kai agaji
Mutum biyar sun mutu a hatsarin helikwaftan ɗaukar marasa lafiya a Libya
Yadda 'yan Somaliya suka gina wa tsohon shugaba ƙasarsu Farmaajo sabon gida
Sake dawo da ainihin martabar Afirka
RSF ta Sudan ta kai hari da jirgi maras matuƙi, ta kashe gomman mutane da yara
Dubban ‘yan kasar Libya sun taru don halartar jana'izar Saif al-Islam Gaddafi
Harin RSF a wani asibiti a Sudan ya kashe mutum 22, ciki har da ma'aikatan jinya
Ghana da Zambia sun ƙulla yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba yayin ziyarar Mahama
Saif al-Islam Gaddafi: An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi
Afirka na fuskantar tarnaƙin bashin dala biliyan 90 a 2026, in ji S&P
Yadda Biteye na Senegal ke amfani da ƙwallon ƙafa don samun waraka ga ƙwaƙwalwa
Sojojin Rasha sun taimaka wajen daƙile hari a filin jirgin saman Nijar: Moscow
'Yanbindiga sun kashe sojojin Libya uku a kusa da kan iyakar Nijar