| Hausa
WASANNI
3 MINTI KARATU
Man City ta ƙara samun dan wasan da zai yi jinya
Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya tabbatar da cewa raunin da ɗan wasan bayansu John Stones ya ji zai kwantar da shi tsawon makonni 10.
Man City ta ƙara samun dan wasan da zai yi jinya
John Stones ɗan asalin Ingila ne mai shekaru 30. / Hoto: AFP / AFP
26 Fabrairu 2025

John Stones ɗan wasan baya na Manchester City zai yi jinyar har makonni 10, bayan raunin da ya samu makon jiya, kamar yadda kocin ƙungiyar Pep Guardiola ya tabbatar.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin Ingila ne, ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan da suka buga da Real Madrid a gasar Zakarun Turai, inda suka yi rashin nasara da ci 1-3.

Yanzu dai ta tabbata cewa Stones zai yi jinyar sama da wata biyu, wanda hakan zai zama ƙarin matsala ga ƙungiyar da kuma kocinsu Guardiola, wanda ya ce ba za a yi wa ɗan wasan tiyata ba.

Ana fatan ɗan wasan da yake buga wa tawagar ƙasar ta Three Lions, zai murmure cikin makonni takwas zuwa 10.

Raunin da Stones ya samu na zuwa ne a lokacin da City ke fama da jerin masu jinya a manyan 'yan wasanta, ciki har da mai tsaron baya Manuel Akanji, wanda ake sa ran zai dawo fili nan kusa bayan shi ma an masa tiyata a baya.

Tawagar Ingila

Ita ma tawagar Ingila labarin bai mata daɗi ba kasancewar Stones zai rasa wasan neman cancantar shiga gasar Kofin Duniya da za su buga da Albania da kuma Latvia, inda sabon koci Thomas Tuchel zai fara jagorantar su.

Yayin da John Stones zai tafi doguwar jinya, kocin Man City ya bayyana cewa ɗan wasansu Oscar Bobb yana dab da komowa, bayan daɗewa yana jinya.

Bobb mai shekaru 21 yana murmurewa daga raunin karaya a ƙafa wanda ya samu yayin atisaye a watan Agustan bara, wanda ya sa shi jinyar kusan watanni 7.

Shi ma gwarzon ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland yana nuna alamun murmurewa don buga wasansu na gaba a gidan Tottenham.

Haaland ɗan asalin Norway ya rasa wasanni biyu da City ta buga saboda rauni a gwiwa yayin wasan City da Newcastle a farkon watan nan.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Toni Kroos ya soki gasar ƙwallo ta Saudiyya game da raina tasirin Ronaldo
Victor Osimhen ya ci ƙwallo ta 200 a rayuwarsa ta wasa
Atletico Madrid ta ce ta cim ma yarjejeniya da Atalanta kan ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman
Real Madrid za ta sake karawa da Benfica a wasan cike gurbi na Gasar Zakarun Turai
Mourinho ya bai wa Kocin Real Madrid haƙuri bayan Benfica ta doke Madrid a Gasar Zakarun Turai
CAF ta dakatar da kocin Senegal da Achraf Hakimi
Cole Palmer na son komawa Man United, Liverpool ba za ta rabu da kyaftin dinta, Virgil van Dijk ba
'Yanwasan Senegal sun samu kyautar kuɗi da fuloti saboda lashe Kofin AFCON
Dubban mutane sun halarci bikin karrama Zakarun Kofin AFCON a Senegal
Real Madrid ta sallami Xabi Alonso, ta nada Alvaro Arbeloa sabon koci
Hukumar CAF ta yi tir da rashin ɗa'a a zagayen kwata-fainal na AFCON 2025
Ɗan wasan Ghana Semenyo ya koma Man City daga Bournemouth kan dala miliyan 87
Yadda ƙarin kuɗaɗen tallafi ke taimaka wa mata ‘yanwasan ƙwallon ƙafa da ke fama da nakasa a Kenya
Wane ne Liam Rosenior, sabon kocin Chelsea?
Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim bayan ya soki shugabancin kungiyar
An sallami Anthony Joshua daga asibiti
Abubuwa 5 game da mai jiran Man United ta ci wasa 5 a jere, wanda ya kwana 452 ba aski
Yadda Tanzania ta tsallaka gaba da maki biyu kacal a gasar AFCON 2025
Hatsarin mota ya rutsa da Anthony Joshua a jihar Ogun ta Nijeriya
AFCON 2025: Za a fara wasannin ƙarshe na matakin rukuni don tantance ƙasashe 16 masu tsallakawa gaba