A hukumance Turkiyya ta ba da izinin shiga ba tare da biza ga 'yan kasar China don yawon bude ido da wucewa, kamar yadda dokar shugaban kasar ta bayyana wacce aka wallafa a ranar Laraba.
Sabuwar manufar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanya wa hannu, ta bai wa maziyartan kasar Sin damar zama a Turkiyya na tsawon kwanaki 90 a cikin ko wace kwanaki 180, wacce za ta fara aiki daga ranar 2 ga watan Janairun 2026.
Manufar matakin shi ne karfafa huldar yawon bude ido da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, biyo bayan karuwar ‘yan China masu shiga Turkiyya.
Alkaluman kididdiga na kasar Turkiyya sun nuna cewa, a shekarar 2024, masu yawon bude ido ‘yan China 410,000 ne suka ziyarci Turkiyya, wanda ya nuna karuwar kashi 65.1 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Yanzu kasar China ta zama daya daga cikin kasuwannin yawon bude ido na Turkiyya da ke saurin bunkasa.
A farkon wannan shekara, jakadan kasar China ya bayyana irin abubuwan da suke jan hankalin ‘yan China zuwa Turkiyya.
"Dumbin abubuwan tarihi, da al'adu, da abubuwan jan hankali da suka shahara a duniya, su ne suke jan hankalin masu yawon bude ido na China zuwa Turkiyya" in ji shi a wani taron da ya gudana a ofishin jakadancin China da ke Ankara.
"Bayan annobar Korona an ga karuwar masu ziyara, kuma Turkiyya ta zama kasuw mafi saurin bunkasa ga baƙi na duniya."
Jakada Jiang ya yi nuni da cewa, ya shaida dadaddiyar wayewar kasar da abubuwan al'ajabi, yana mai jaddada karuwar huldar al'adu da yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu.
Jami'ai na sa ran cewa, ba tare da biza ba, zai kara habaka yawon bude ido 'yan China, da tallafawa tattalin arzikin cikin gida, da ƙarfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Dangantakar Turkiyya da China na kara karfafa ta hanyar fadada harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da mu'amalar al'adu, tare da karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da diflomasiyya.


























