Hukumar tsaron Nijar ta ce an ƙaddamar da farautar nemo ‘yanbindigan da ke da hannu a harin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla jami’an tsaron ƙasar 13 a yankin Tillaberi da ke yammacin ƙasar.
A cikin wata sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Nijar ta fitar kana aka karanto ta gidan talabijin na ƙasa, ta ce ‘‘wasu gungun ‘yanbindiga ne suka kai wa jami'an rundunar tsaron ƙasa ta Nijar (National Guard) a wani harin ta’addanci.’’
Nijar na yawan fama da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh, waɗanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane cikin shekaru goma da suka wuce.
Aƙalla jami'an tsaro 13 ne suka mutu, yayin da wasu 20 suka jikkata a harin da aka kai ranar Alhamis a ƙauyen Sanam, a cewar alƙaluman farko da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar.
Yaƙi da ayyukan ta’addanci
Jami'an tsaron da aka kai wa harin na cikin rundunar da ke gudanar da aikin yaƙi da ta'addanci a ƙasar.
Ƙasar Nijar dai, ta jima tana fama da matsalolin rashin tsaro a yankuna daban-daban sakamakon ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma safarar haramtattun kayayyaki ta kan iyakoki.
Jami'an tsaron ƙasar na gudanar da samame akai-akai domin tarwatsa sansanonin 'yanbindiga, da dakile hanyoyin samar musu da kayan aiki da kuma rage safarar haramtattun kayayyaki, musamman a yankunan da ke kan iyakoki da wuraren da ke da koguna.
A 'yan shekarun nan, hukumomin Nijar sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro na haɗin-gwiwa a yankuna daban-daban, tare da mai da hankali kan dakile kutsen masu ɗauke da makamai, da safarar man fetur ba bisa ƙa'ida ba, da kuma yaɗuwar makamai da na'urorin fashewa.
Ayyukan soji na baya-bayan nan na nuna ci gaba da ƙoƙarin hukumomin ƙasar na matsa lamba kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da kuma hanyoyin sadarwar masu aikata laifuka a faɗin Nijar.















