| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Kim Jong-un ya bayar da umarnin tura makaman nukiliya zuwa sassan ayyukan soji
Koriya ta Arewa ta yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri daga ƙasashen waje na ƙalubalantar matsayinta na ƙasa da ta mallaki makaman nukiliya, zai zama tamkar ayyana mata yaƙi ne kai tsaye.
Kim Jong-un ya bayar da umarnin tura makaman nukiliya zuwa sassan ayyukan soji
Kim ya yi gargadi kan a guji kalubalantar matsayin Koriya ta Arewa na mallakar makaman nukiliya. / AP
 

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya bayyana cewa ya kamata ƙasar ta mayar da hankali wajen tura makaman nukiliya na yaƙi zuwa sassa daban-daban na ayyukan soji, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da faɗaɗa ƙarfin samar da sinadaran nukiliya a ƙasar, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran ƙasar, KCNA ya ruwaito.

Kim ya bayyana haka ne yayin ziyarar duba cibiyoyin samar da sinadaran nukiliya da cibiyoyin binciken makamai, inda ya jaddada cewa ba za a iya kawar da matsayin Koriya ta Arewa ta zama ƙasa wadda ta mallaki makaman nukiliya ko kuma tattaunawa a kai da sauran ƙasashe ba.

Masu AlakaTRT Afrika - Shugaban Koriya ta Arewa ya je kallon gwajin makami mai linzami mai iya ɗaukar nukiliya

“Ƙarfinmu na nukiliya ya bayyana a zahiri,’’ kamar yadda kafar KCNA ta ruwaito Kima yana cewa” inda ya ƙara da cewa matsayin ƙasar na ikon cin gashin kanta ba zai sauya ba saboda kalaman ƙasashen waje ko kiraye-kirayen dakatar da shirin nukiliyarta.

Tura makaman nukiliya zuwa fannoni daban-daban na yaƙi

Kim ya umarci hukumomin sojin ƙasar da su ‘‘mayar da hankali wajen amfani da makaman nukiliya na yaƙi a fannoni daban-daban, domin gudanar da ayyuka da manufofi mabambanta.’’

Ya kuma yaba da ci gaban da aka samu a samar da manyan makaman nukiliya, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar nasara wajen aiwatar da manufar ƙasar kan makaman nukiliya.

Shugaban na Koriya ta Arewa ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri daga ƙasashen waje na ƙalubalantar ƙasar na mallakar makaman nukiliya, wanda ƙundin tsarin mulkin ƙasar tanada a shekarar 2023, za a ɗauki hakan a matsayin ayyana yaƙi kai tsaye.

Ya sake jaddada cewa ƙasar ba za ta taɓa yin watsi da makaman nukiliyarta ba, waɗanda ya bayyana a matsayin babbar hanyar tabbatar da tsaron ƙasa.

“Mallakar makaman nukiliyarmu wani zaɓi ne da ba za a iya sauyawa ba, muddin akwai ƙasashe masu mugun nufi da ke amfani da makaman nukiliya domin cim ma burinsu na mamaye duniya,” in ji Kim.

Tun daga shekarar 2006, Koriya ta Arewa ta ke gudanar da gwaje-gwajen makaman nukiliya guda shida a ƙarƙashin ƙasa, inda ta gudanar da gwajin da ya fi kowanne ƙarfi a shekarar 2017.

A watan Agusta, ministan tsaron Koriya ta Kudu ya bayyana cewa wasu ƙididdigar masu zaman kansu sun nuna cewa Koriya ta Arewa na iya mallakar manyan makaman nukiliya tsakanin 80 zuwa 120.

Sai dai ya bayyana cewa alkaluman sun fito ne daga cibiyoyin bincike masu zaman kansu, kuma hukumomin leƙen asirin ƙasashen ba su tabbatar da sahihancinsu ba.