AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Wata sanarwar daga rundunar sojin Ghana (GAF) ta ce an yi kamen  ne ranar juma’a 31 ga watan Oktobar shekarar 2025, bayan an sami kiran neman ɗauki daga jirgin.
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Rundunar ta ce ta miƙa 'yan Nijeriyar ga hukumomin da ya kamata
11 awanni baya

Rundunar sojin ruwan Ghana ta kama ‘yan Nijeriya  da suka yi yunƙurin balaguro a ɓoye a cikin wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar ƙasar Panama, MV Grand Venus,  a tashar jiragen  ruwa ta Tema.

Wata sanarwa daga rundunar sojin Ghana (GAF) ta ce an yi kamen ne ranar Jumma’a 31 ga watan Oktoban shekarar 2025, bayan an samu kiran neman ɗauki daga jirgin.

Bincike ya nuna cewa mutanen sun shiga jirgin ruwan ne a asirce a lokacin da ya tsaya a tashar jiragen ruwa ta Nijeriya da ke Legas.

“Rundunar sojin ruwan Ghana a ranar Jumma’a , 31 ga watan Oktoban shekarar 2025, ta kama mutum 10 masu tafiya a ɓoye cikin wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Panama Grand Venus a  bayan an samu kiran neman ɗauki,” in ji sanarwar.

Bayan kamen, rundunar sojin ruwan Ghana ta raka jirgin ruwan zuwa tashar jiragen ruwan inda ta miƙa waɗanda ake zargin ga hukumomin da lamarin ya shafa ciki har da masu kula da tashar jiragen ruwa da hukumar shige da ficen Ghana da kuma ‘yan sandan ruwa domin ƙarin bincike.

Rundunar sojin ta tabbatar wa jama’ar ƙasar cewa za ta yi ƙarin bayani yayin da ake ci gaba bincike.

“Rundunar sojin ruwan Ghana tana so ta tabbatar wa mutane cewa za ta yi ƙarin haske yayin da bincike ke ci gaba,” in ji sanarwar.